Bayan Hadarin Kano Pillars, Mutane Kusan 20 da Ke Hanyar zuwa Abuja Sun Gamu da Ajali

Bayan Hadarin Kano Pillars, Mutane Kusan 20 da Ke Hanyar zuwa Abuja Sun Gamu da Ajali

  • Wata motar bas mai ɗaukar fasinjoji 18 ta gamu da mummunan hatsari a yankin ƙaramar hukumar Riyom a jihar Filato
  • Mai magana da yawun hukumar kiyaye haɗurra (FRSC), Peter Yakubu ya ce dukkan fasinjojin motar da direba sun mutu
  • Ya ce mutum 18 suka mutu nan take a wurin da hatsarin ya auku yayin da ragowar mutum ɗaya ya cika a gadon asibiti

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jos, Jihar Plateau - Akalla mutane 19 ne suka mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a yankin Hawan Kibo da ke karamar hukumar Riyom ta jihar Filato.

Rahotanni sun bayyana cewa Hawan Kibo, wanda ke dab da shiga Jos, babban birnin jihar Filato, yana da tazarar kilomita 60 daga babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Ana kukan lantarki, ruwa ya karya gadar da ta haɗa ƙauyuka sama da 50

Jami'an hukumar FRSC.
Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 19 da ke hanyar zuwa Abuja Hoto: Federal Road Safety Corps Nigeria
Asali: Facebook

Kakakin hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen Filato, Peter Yakubu, ya tabbatar da faruwar haɗarin ga ƴan jarida a Jos, kamar yadda Leadership ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dukkan fasinjojin motar sun mutu

Peter Yakubu ya bayyana cewa dukkan fasinjojin da ke cikin motar da ta yi haɗarin sun riga mu gidan gaskiya.

''Babu wanda ya tsira daga hatsarin, mutum daya tilo da aka kai asibiti daga baya ya rasu. Fasinjoji 18 suka mutu nan take yayin da dayan ya mutu a asibiti," in ji shi.

FRSC: An kai gawarwaki asibiti a Jos

Wata ma’aikaciya a asibitin Riyom Trauma ta shaidawa manema labarai cewa an kawo gawarwakin wadanda suka mutu.

Malamar asibitin ta ce:

"Dukkan waɗanda aka kawo mana sun riga sun mutu, yanzu da nake magana da ku an maida gawarwakin zuwa ɗakin adana gawa a Jos saboda rashin wuta a nan Riyom."

Kara karanta wannan

Barayi sun tasa Abuja a gaba, majalisa ta gayyato Ministan Tinubu da DSS

Ma’aikatan asibitin sun kara da cewa motar da lamarin ya shafa ta taso ne daga jihar Adamawa zuwa Abuja lokacin da hatsarin ya afku.

Mutum 6 sun mutu a hatsarin Oyo

A wani rahoton kuma aƙalla mutane shida ne aka tabbatar da rasuwarsu yayin da wasu mutum biyar suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a jihar Oyo.

Hatsarin motan ya auku ne a kan hanyar Akanran a yankin Ona Ara a ƙaramar hukumar Ibadan da sanyin safiyar ranar Litinin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262