Shugaba Tinubu Ya Gana da Gwamna kan Mutuwar Mutane 181, Bayanai Sun Fito

Shugaba Tinubu Ya Gana da Gwamna kan Mutuwar Mutane 181, Bayanai Sun Fito

  • Mai girma shugaban ƙasa ya karɓi bakuncin gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi a fadar Aso Villa a ranar Talata
  • Gwamnan ya yi wa Bola Ahmed Tinubu bayanin halin da ake ciki bayan fashewar tankar man da ta yi sanadin mutuwar mutane 181
  • Ɗanmodi ya yabawa Shugaba Tinubu bisa tura tawaga ta musamman zuwa Jigawa bayan faruwar mummunan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Damadi a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja.

Wannan ziyara da gwamnan ya kai wa ahugaba Tinubu ta maida hankali ne kan fashewar tankar mai da ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 150 a Jigawa.

Kara karanta wannan

Gwamna Dikko ya kere gwamnoni, an ba shi lambar yabo ta kasa da kasa a Faransa

Gwamna Namadi da Tinubu.
Gwamna Namadi ya yiwa shugaban kasa bayanin halin da ake ciki bayan fashewar tanka a Jigawa Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau Gwamna Namadi ya yi amfani da wannan dama wajen yi wa shugaba Tinubu barka da dawowa daga hutun da ya tafi ƙasashen ƙetare.

Dalilin ganawar Namadi da Bola Tinubu

Sai dai babban maƙasudin ganawarsa da Tinubu shi ne yiwa shugaban cikakken bayani kan lamarin gobarar tankar da ta laƙume rayukan mutane 181 kawo yanzu.

Gwamna Namadi ya ce haɗarin tankar ya halaka mutum 181, ya bar wasu mutane akalla 80 kwance a asibiti suna jinya, sannan ya taɓa iyalai sama da 200 a Jigawa.

Da yake zantawa da da ƴan jaridar gwamnati bayan ganawa da Tinubu, Umar Namadi ya godewa shugaban bisa tura wakilai bayan faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

Mutane sun shiga matsala yayin da ruwa ya mamaye garuruwa 25, an samu bayanai

Gwamna Namadi ya yabawa Shugaba Tinubu

"Al'ummar Jigawa sun ji daɗin wannan mataki na tura wakilai cikin gaggawa da shugaba Tinubu ya ɗauka," in ji shi.

Umar Namadi ya kuma yi wa shugaban kasa bayani kan kokarin da jihar ke yi, wanda ya hada da biyan kudaden jinya na wadanda ke kwance da bayar da tallafi ga iyalan da suka rasa ƴan uwansu.

Da aka tambaye shi dalilin ƙaruwar adadin waɗanda suka mutu, gwamnan ya ba da amsa da cewa, "Allah kuke tuhuma ko kuma ni?"

Gwamnonin Arewa sun tallafawa Jigawa

A wani rahoton kuma yayin da ake cigaba da jimamin rasa rayuka a jihar Jigawa, gwamnonin Arewacin Najeriya sun ba da tallafi mai tsoka.

Shugaban gwamnonin, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya jajantawa gwamnatin jihar da al'umma kan wannan iftila'i da ya afku.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262