Ana Kukan Lantarki, Ambaliya Ta Karya Gadar da Ta Haɗa Ƙauyuka Sama da 50

Ana Kukan Lantarki, Ambaliya Ta Karya Gadar da Ta Haɗa Ƙauyuka Sama da 50

  • An samu mummunar ambaliyar ruwa a wasu kauyuka na karamar hukumar Ibarapa ta Gabas a jihar Oyo da ke Kudancin Najeriya
  • Rahotanni sun nuna cewa an tafka ruwan sama mai karfi ne a tsawon kwanaki biyu inda lamarin ya jawo barna mai muni
  • Mutanen yankin da abin ya shafa sun fara kira ga shugabanni da su kawo musu dauki domin magance matsalolin da lamarin ya jefa su ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Oyo - An samu mummunar ambaliyar ruwa a jihar Oyo bayan an shafe kwanaki ana tafka ruwan sama.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a wani yanki na ƙaramar hukumar Ibarapa ta Gabas ta jihar Oyo.

Kara karanta wannan

"Sun zama maboyar miyagu:" FCTA ta bayar da wa'adin kammala gine gine a Abuja

Jihar Oyo
Ambaliya ta yi rusa gada a Oyo. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mutanen garin sun fara kira ga gwamnati da sauran al'umma domin a kawo musu agaji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gadar da ta haɗa ƙauyuka 50 da rushe

Ambaliyar ruwa ta rusa gadar Ipin da ta haɗa ƙauyuka sama da 50 a karamar hukumar Ibarapa ta Gabas a jihar Oyo.

Lamarin ya faru ne biyo bayan ruwan sama mai karfi da aka tafka a ranakun Juma'a da Asabar a karamar hukumar.

Wani mazaunin garin ya bayyana cewa a yanzu haka lamura sun tsaya cak saboda mutane ba su da wata hanyar zirga-zirga.

"Mun yi imani da cewa komai daga Allah ya ke, amma ba mu taba ganin ruwa mai karfi irin wannan ba.
Gadar da ta rushe ta haɗa ƙauyuka sama da 50 a karamar hukumar Ibarapa ta Gabas."

-Wani mazaunin Ibarapa ta Gabas

Kara karanta wannan

Mutane sun shiga matsala yayin da ruwa ya mamaye garuruwa 25, an samu bayanai

An bukaci taimako kan ambaliyar ruwa

Daily Post ta wallafa cewa mutanen garin sun bukaci taimako daga shugaban karamar hukumar Ibarapa ta Gabas, Hon. Kazeem Arogundade.

Haka zalika sun yi kira ga dan majalisa mai wakiltarsu a majalisar dokokin jihar, Hon. Adebo Ogundoyin domin kawo musu agaji.

Ambaliya ta yi barna a gonaki

A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni sun nuna ambaliyar ruwa ta yi kaca-kaca da amfanin gonakin al'umma a wasu yankuna da ke jihohin Kebbi da Neja.

Hukumar N-HYPPADEC ta miƙa sakon jaje ga waɗanda ibtila'in ya shafa tare da yabawa matakin gwamnatin tarayya na ware N3bn.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng