Gwamna Dikko Ya Kere Gwamnoni, An Ba Shi Lambar Yabo Ta Kasa da Kasa a Faransa

Gwamna Dikko Ya Kere Gwamnoni, An Ba Shi Lambar Yabo Ta Kasa da Kasa a Faransa

  • An ba gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda lambar yabo a ɓangaren wasanni a birnin Faris na ƙasar Faransa
  • Kungiyar OJB ta karrama gwamnan ne bisa irin gudummuwar da yake bayarwa wajen bunƙasa harkokin wasanni a jihar Katsina
  • Kwamishinan matasa da wasanni na Katsina, Hon Lawal Aliyu Zakari ya jagoranci tawagar da ta wakilci Radda a Faransa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya samu lambar yabo kan gudummuwar da yake bayar wa a ɓangaren wasanni.

Kungiyar OJB Media Network ta karrama Gwamna Radda da lambar yabo ta wasanni da ake kira da, "Nigeria France Sports Award."

Malam.Dikko Radda.
An karrama Gwamna Dikko Radda da lambar yabo a bangaren wasanni Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Sakataren watsa labaran mai girma gwamnan, Ibrahim Kaula Muhammed ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamna a Arewa ya hango haɗari, ya rufe manyan makarantun kuɗi nan take

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Radda ya samu lambar yabo

A cewarsa, kungiyar ta ba gwamnan wannan lambar yabo ta ƙasa da ƙasa ne domin jinjina masa bisa yadda yake ba da gudummuwa wajen ci gaban harkokin wasanni a jihar Katsina.

An gudanar da taron karrama mai girma gwamna a ɗakin taron Bateau Leuisiane Belle Boat da ke birnin Faris na ƙasar Faransa.

Sai dai Malam Dikko Raɗɗa bai samu halarta ba, amma ya tura tawaga karkashin jagorancin kwamishinan harkokin matasa da wasanni, Hon. Lawal Aliyu Zakari.

Sauran ƴan tawagar sun haɗa da shugaban kwamitin wasanni na majalisar dokokin Katsina, Sani Mustapha Bello da shugaban makarantar kwallon ƙafa ta Katsina, Ahmed Mohammed.

Dalilin karrama Dikko Radda a Faransa

Ibrahim Kaula Mohammed ya ce:

"Ƙungiyar OJB ta karrama Mai girma gwamnan Katsina Malam Dikko Radda da lambar yabon ta wasanni."

Kara karanta wannan

Gwamna a Arewa ya shiga layi, ya sanar da sabon albashin da zai iya biyan ma'aikata

"Gwamna Radda ya samu wannan lambar yabo ta ƙasa da ƙasa ne saboda gudummuwar da yake bayar wa a ɓangaren wasanni a jihar Katsina."

Radda ya rufe makarantu lafiya na kudi

A wani rahoton kuma Mai girma Dikko Umaru Radda ya ba da umarnin soke lasisi da rijistar makarantun lafiya na kuɗi a faɗin jihar Katsina.

Gwamnan ya ce bincike ya nuna galibin makarantun lafiya masu zaman kansu ba su da inganci wanda hakan haɗari ne ga lafiyar jama'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262