"Sun Zama Maboyar Miyagu:" FCTA Ta Bayar da Wa'adin Kammala Gine Gine a Abuja
- Hukumar gudanarwar babban birnin tarayya Abuja ta ce za ta fara rushe wasu gine-gine da mamallakansu su ka ki kammalawa
- A wata sanarwa da wani jami'in FCTA, Felix Obuah ya sanyawa hannu, ya ce an ba masu gine-ginen da ba a karasa ba wa'adin karasawa
- Ya bayyana dalilin da ya sa aka dauki matakin, wanda a cewarsa ya jibanci kyautata tsaron rayuka da dukiyoyin mazauna Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Hukumar gudanarwar birnin tarayya Abuja ta ba mutanen da ke da gidajen da ba a kammala ba wa’adin watanni uku su kammala su.
Hukumar ta yi barazanar rushe dukkanin wani gida da aka ki kammala shi a kwaryar birnin babban birnin tarayyar a wannan lokaci.
Punch ta wallafa cewa umarnin mai kunshe da wa'adin kammala kwangayen na kunshe a wata sanarwa da jami’in hukumar FCTA, Felix Obuah ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gano karuwar kwangaye a Abuja
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa hukumar birnin tarayya Abuja ta ce an gano karuwar gine-gine da ba a kammala ba bisa ka’ida ba a birnin.
Jami’in hukumar FCTA, Felix Obuah ya bayyana cewa hakan ta sa aka ga dacewar bayar da lokacin ga mamallaka gidajen da su kammala su ko a ruguje su.
Abuja: Dalilin bayar da wa'adin kammala kwangayen
Hukumar gudanarwar Abuja ta ce gine-ginen da ba a kammala ba kan zama maboyar masu aikata miyagun laifuka a yankin.
"Hukumar ta gano cewa ana amfani da wadannan gine-gine da filaye wajen boye marasa gaskiya wanda ke zama babbar barazanar tsaro ga mazauna yankin," cewar Felix Obuah.
FCTA ta kaddamar da rushe gidaje a Abuja
A wani labarin kun ji cewa hukumar gudanarwar birnin tarayya Abuja ta bayyana cewa za ta fara rusa wasu daga cikin gidajen da aka gina a birnin ba bisa ka'ida ba domin tsaftace birnin.
Hukumar, karkashin jagorancin Ministan Abuja, Nyesom Wike ne ta bayyana cewa ba za ta lamunci a ci gaba da gina haramtattun gine-gine a sassan babban birnin Abuja ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng