Mutane Sun Shiga Matsala da Ruwa Ya Mamaye Garuruwa 25, An Samu Bayanai

Mutane Sun Shiga Matsala da Ruwa Ya Mamaye Garuruwa 25, An Samu Bayanai

  • Ambaliyar ruwa ta ci kauyuka akalla 25 da ke gaɓar Kogin Neja a kananan hukumomi uku da ke jihar Edo
  • Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne sakamakon sako ruwa daga madatsar Lagdo ta ƙasar Kamaru
  • An ce ruwa ya cinye wasu kauyukan gaba ɗaya yayin da mazauna suka koma rayuwa a sansanonin ƴan gudun hijira

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Edo - Rahotanni sun bayyana cewa akalla kauyuka 25 da ke gabar kogin Neja ne ruwa ya mamaye a jihar Edo.

Wannan mummunar ambaliya ta faru ne sakamakon sakin ruwa da babbar madatsar ruwar Lagdo da ke ƙasar Kamaru.

Taswirar Edo.
Ambaliyar ruwa ta ci kauyuka akalla 25 a jihar Edo Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Kananan hukumomin da abin ya shafa a gabar kogin Neja sun hada da Etsako ta Gabas, Etsako ta tsakiya da kuma Esan ta Kudu maso Gabas, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Ana kukan lantarki, ruwa ya karya gadar da ta haɗa ƙauyuka sama da 50

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane mataki gwammati ta ɗauka?

Jami'in da ke kula da sashin kai agajin gaggawa a ƙaramar hukumar Esan ta Kudu maso Gabas, Ojimah Christopher ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce ruwa ya mamaye gaba ɗaya kauyuka 25, inda ya kara da cewa mazauna kauyukan da lamarin ya shafa sun koma sansanonin ƴan gudun hijira.

Mista Ojimah ya ce a halin yanzu mutane sun cika sansanin ƴan gudun hijaran da gwamnati ta buɗe a ƙaramar hukumar.

A cewarsa akwai wasu kauyuka da ruwan ya cinye gaba ɗaya kamar kauyen Ifeku, inda ruwan ya yi awon gaba da kadarori da dabbobin mazauna garin.

Ambaliyar ruwa ta yi ɓarna a Edo

Wani mazaunin yankin da lamarin ya shafa, John Odaku ya ce ruwa ya mamaye gonakinsu da suka noma doya, rogo, gyada da sauran su, ya tafi da amfanin gonakin.

Kara karanta wannan

Hisbah ta ayyana neman kwamishina ruwa a jallo kan zargin lalata a Kano

"Muna gani ruwa ya tafi da amfanin gonakinmu saboda ba za mu iya ceto su tare da dabbobin mu ba," in ji shi.

Ya yi kira ga gwamnatin jiha da ta Tarayya da su kawo musu dauki, ganin cewa gwamnatin ƙaramar hukumar tana iya bakin ƙoƙarinta, The Nation ta ruwaito.

Kogi: Ambaliya ta tarwatsa garuruwa 200

A wani rahoton kuma ambaliyar ruwa ta ci garuruwa da dama a kananan hukumomin jihar Kogi, kimanin mutane miliyan biyu sun rasa gidajensu

Gwamnatin jihar Kogi ta buƙaci a kawo mata ɗauki domin tallafawa waɗanda wannan mummunan ibtila'i ya rutsa da su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262