Gwamna a Arewa Ya Hango Haɗari, Ya Rufe Manyan Makarantun Kudi Nan Take
- Mai girma Dikko Umaru Radda ya ba da umarnin soke lasisi da rijistar makarantun lafiya na kuɗi a faɗin jihar Katsina
- Gwamnan ya ce bincike ya nuna galibin makarantun lafiya masu zaman kansu ba su da inganci wanda hakan haɗari ne ga lafiyar jama'a
- Mai taimakawa gwamnan kan harkokin lafiya, Umar Mammada ya ce wannan umarni zai fara aiki nan take har sai an gama bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - Gwamna Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya ba da umarnin rufe dukkan makarantun kiwon lafiya masu zaman kansu da ke aiki a faɗin jihar Katsina.
Mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin lafiya, Umar Mammada ne ya sanar da hakan a wata hira da manema labarai ranar Litinin a Katsina.
A rahoton Punch, Umar ya ce gwamnatin Katsina ta gano cewa an samu karuwar makarantun horas da malaman lafiya marasa inganci a ƴan shekarun nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin Dikko na rufe makarantun lafiya na kudi.
"Binciken da gwamnati ta yi ta hannun ma'aikatar lafiya ya nuna akwai damuwa kan yadda wasu makarantun lafiya na kudi ke tafiyar da aikinsu ba tare da yin rijista ba.
"Wasu daga cikin ire-iren waɗannan makarantu ba su cika ƙa'idojin doka na fara aiki a matsayin makarantun koyar da aikin lafiya ba, wanda hakan ba karamin haɗari ba ne ga rayuwar jama'a.
"Bisa la'akari da haka ne Mai girma gwamna ya bayar da umarnin rufewa tare da soke rajista da lasisin dukkan makarantun kiwon lafiya na kudi a Katsina."
- Umar Mammada.
Gwamna ya faɗi matakin da zai ɗauka
Hadimin gwamnan ya bukaci makarantu masu zaman kansu, ma'aikata da sauran al'ummar Katsina su rungumi wannan umarni saboda ya zama dole.
Umar ya jaddada cewa gwamnati za ta yi amfani da wannan dakatarwa wajem gyara makarantun kudi da yi masu sabuwar rijista a hukumance.
Gwamnan Katsina na shirin karya farashin abinci
A wani rahoton kuma gwamnatin Katsina ta amince da kawo shirin sayar da abinci a farashi mai sauki a dukkan kananan hukumomin jihar.
Dikko Umamar Radda ya tabbatar da cewa za a kafa shangunan ne domin sayar da abinci da ake amfani da shi a yau da kullum.
Asali: Legit.ng