Yan Bindiga Sun Shiga Gari Sun Bude Wuta, da Dama Sun Mutu

Yan Bindiga Sun Shiga Gari Sun Bude Wuta, da Dama Sun Mutu

  • Ana fargabar samun asarar rayuka da dama da wasu yan bindiga suka bude wuta kan al'umma a karamar hukumar Akwa ta Kudu
  • An ruwaito cewa lamarin ya faru ne a kusa da kasuwar Nwochichi da miyagun suka fito a cikin mota kirar Jeep suka fara sakin wuta
  • Kakakin yan sanda a jihar Anambra, Tochukwu Ikenga ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya fadi matakin da suka dauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Anambra - Mutanen karamar hukumar Akwa ta Kudu a jihar Anambra sun samu kansu a cikin wani mummunan yanayi bayan harin yan bindiga.

An ruwaito cewa wasu yan bindiga ne suka bude wuta kan al'umma kuma da dama sun rigamu gidan gaskiya.

Kara karanta wannan

Jigawa: Adadin wadanda suka mutu a fashewar tanka ya haura 175, bayanai sun fito

Anambra
An kai hari a Anambra. Hoto: Legit
Asali: Original

Rahoton Channels Television ya nuna cewa rundunar yan sanda ta dauki mataki bayan faruwar lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan bindiga sun kai hari a jihar Anambra

Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu miyagu sun kai hari kan mutane a karamar hukumar Akwa ta Kudu a Anambra.

Shaidar gani da ido ya bayyana cewa mutanen sun fito ne a mota kirar Jeep suka fara harbi kan mai uwa da wabi.

Mutane 10 sun mutu bayan kai harin

Haka zalika an ruwaito cewa akalla an tattara gawar mutane goma a lokacin da yan bindigar suka tafi.

Sai dai har yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka mutu ba saboda an tafi da wasu wuraren neman magani.

Bayanin rundunar yan sanda

Punch ta wallafa cewa rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa ta tura karin runduna ta musamman domin tabbatar da kama miyagun.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun tunkari Abuja da tsakar rana, sun fafata da yan sanda

Kakakin yan sanda a Anambra, Tochukwu Ikenga ya kara da cewa akwai buƙatar mutane su ba su bayanan da za su taimaka musu wajen kama yan bindigar.

An fatattaki yan bindiga a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa jami'an yan sanda sun fafata da wasu miyagun yan bindiga da suka tunkari birnin tarayya Abuja da tsakar rana.

Rundunar yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta ce jami'ai sun kwato wasu daga cikin makaman miyagu yan bindigar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng