Kwana Ya Ƙare: Hadimin Tsohon Minista Ya Mutu a 'Otel' a Abuja, An Gano Abin da Ya Faru

Kwana Ya Ƙare: Hadimin Tsohon Minista Ya Mutu a 'Otel' a Abuja, An Gano Abin da Ya Faru

  • Hadimin tsohon minista, Ndifreke Mark ya riga mu gidan gaskiya bayan dawowa daga wurin bauta a birnin tarayya Abuja
  • Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ne ya tabbatar da rasuwar marigayi Mark ranar Lahadi da ta gabata
  • Ya ce hadiminsa ya rasu ne a wani ɗakin otal tare da wani mutumi wanda yanzu haka ƴan sanda na tsare da shi domin bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ndifreke Mark, mataimaki na musamman ga tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya riga mu gidan gaskiya.

Fani-Kayode ya ce marigayin ya bar gidansa da sanyin safiya domin halartar taro a cocin Katolika da ke Asokoro a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

"Ka da ku tsaya baya": Gwamna ya fito ya ba matasan Najeriya muhimmiyar shawara

Femi Fani-Kayode da Mark.
Hdiman Fani Kayode ya riga mu gidan gaskiya a otal a Abuja Hoto: Femi Fani-Kayode
Asali: Facebook

A cewarsa, bayan kammala taron a coci ne Ndifreke Mark ya koma wani ɗaƙi da ya kama a Otal na Mildy Lodge a Garki, Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon ministan ne ya bayyana rasuwar hadiminsa a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadin da ta gabata.

Tsohon Minista ya faɗi abin da ya faru

"Mun ɗauki shekaru sama da 34 tare. Ƴan sanda sun ce Mark ya kama ɗaki a otal din inda ya shafe tsawon lokaci a ɗakin tare da wani mutumi, daga baya ya yanke jiki ya faɗi a gaban baƙonsa.
"Daga nan aka garzaya da shi asibiti a Asokoro amma likitoci suka tabbatar da rai ya yi halinsa. Yanzu haka dai ƴan sanda sun tafi da wannan mutumin da suke tare a otal.

- Fani-Kayode.

Yan sanda za su gudanar da bincike

Kara karanta wannan

Kwana ya ƙare: Wani babban ɗan sanda ya mutu cikin ofis, an faɗi abin da ya faru

Tsohon minstan ya jaddada buƙatar gudanar da bincike mai zurfi da gwaje-gwajen gawa domin gano musabbabin rasuwar Ndifreke Mark.

Ya ƙara da cewa tuni ƴan sandan Abuja suka kama mai ba da ɗakuna kuma sun bincike manaja da mamallakin otel din , sannan sun rufe ɗakin da lamarin ya faru.

Fani-Kayode ya yi jimamin wannan rashi, inda ya bayyana marigayin a matsayin ma'aikaci mai ladabi da biyayya da kuma amana.

Yan jarida 2 da ke aiki a majalisa sun rasu

A wani rahoton kuma wasu kwararrun ƴan jarida biyu da ke aiki a majalisar tarayya, Mr. Elijah Olaluyi da Malam Mohammed Adamu sun riga mu gidan gaskiya.

Kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya yi ta'aziyya ga iyalan ƴan jaridar tare da addu'ar Allah ya ba su haƙuri.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262