'Gida bai Koshi ba': TCN Ta Lissafa Kasashe 3 da Najeriya Ke ba Wutar Awanni 24

'Gida bai Koshi ba': TCN Ta Lissafa Kasashe 3 da Najeriya Ke ba Wutar Awanni 24

  • Kamfanin TCN ya bayyana cewa Najeriya na samar da wutar lantarki ta awanni 24 ga kasashen Togo, da Benin, da kuma Nijar
  • Shugaban kamfanin, Sule Abdulaziz ya ce kasashen na biyan kudin wutar da suka sha don haka suke samun wutar babu daukewa
  • Game da durkushewar tashar wutar lantarki da ake fama da ita a Najeriya, Sule Abdulaziz ya ce bai kamata a dorawa TCN laifi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kamfanin da ke kula da lantarki na Najeriya (TCN) ya ce kasar na samar da wuta ta awanni 24 ga kasashen Togo, Benin da Nijar.

Wannan dai na zuwa ne a lokacin da 'yan Najeriya ke fama da rashin wuta sakamakon durkushewar babbar tashar wutar.

Kara karanta wannan

Bayan kara kudin fetur, Tinubu ya shirya kakabawa 'yan Najeriya wani sabon haraji

Kamfanin TCN ya yi magana kan kasashen da Najeriya ke samarwa wuta ta awa 24
TCN ya bayyana lokacin da Najeriya za ta samu daidaituwar wutar lantarki. Hoto: Anton Petrus
Asali: Getty Images

Kasashen da Najeriya ke ba wutar lantarki

A zantawarsa da Channels TV a ranar Lahadi, shugaban kamfanin TCN, Sule Abdulaziz ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Muna samar da wutar lantarki ga Togo, Benin da Nijar. Suna samun wuta ta awanni 24 daga Najeriya kuma suna biyan kudin wutar da suka sha."

Da aka tambaye shi ko 'yan Najeriya na samun irin wannan wutar ta awa 24, Sule Abdulaziz ya ce abokan hulda da ke 'Band A' na samu.

Matsalolin samar da lantarki a Najeriya

Shugaban TCN ya ce:

"Yan Najeriya ma na samun wuta ta awannin 24; amma ba kowa ke samu ba. Wadanda ke karkashin tsarin Band A suna samun wutar sama da awa 20."

Sule Abdulaziz ya ce kowane kamfanin DisCo na da abokan hulda da ke karkashin Band A kuma hakkinsu ne a ba su wuta ta awa 22 zuwa 24.

Kara karanta wannan

An shiga duhu: Wutar lantarkin Najeriya ta sake rikicewa a karo na uku cikin mako guda

Ya kuma ce bai kamata a dorawa kamfanin TCN laifi kan durkushewar tashar wutar kasar ba.

Sai dai shugaban na TCN ya ce yana da yakinin cewa nan da shekaru biyar za a samu wadatacciyar wutar lantarki a fadin Najeriya.

Tashar lantarki ta sake samun matsala

A wani labarin, mun ruwaito cewa babbar tashar wutar lantarkin Najeriya ta sake samun matsala a karo na uku, lamarin da ya kara jefa 'yan kasar a cikin duhu.

Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa samar da wutar ya ragu zuwa megawatt 47 daga megawatt 3,968 da misalin karfe 9 na safiyar ranar Asabar, 19 ga Oktoba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.