Rundunar Yan Sanda Ta Fusata, Ta Gargaɗi Masu Daukar Doka a Hannu

Rundunar Yan Sanda Ta Fusata, Ta Gargaɗi Masu Daukar Doka a Hannu

  • Rundunar yan sandan Najeriya ta yi tir da yadda jama'a ke daukar doka a hannu idan an kama wadanda ake zargi da laifi
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya bayyana haka bayan samun karuwar masu daukar doka a hannu
  • Kakakin rundunar yan sandan na kasa ya ce akwai matsaloli da dama tattare da hukunta wadanda aka kama ba tare da bin doka ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Rundunar yan sandan kasar nan ta bayyana rashin dacewar yadda jama'a ke hukunta wadanda aka kama bisa zargin aikata laifuffuka.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shiga gari sun bude wuta, da dama sun mutu

Jami'in hulda da jama'a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi da ta bayyana haka ya kuma yi takaicin yadda ake samun karuwar masu daukar doka a hannu.

Police
Yan sanda sun koka da yadda jama'a ke daukar doka a hannu Hoto: Adejobi Olumuyiwa
Asali: Facebook

Tashar Trust TV ta tattaro kakakin rundunar yan sandan na kasa na cewa bai dace jama'a su rika take doka, su na hukunta mutanen da aka kama bisa zargin aikata laifi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Illar daukar doka a hannu" - Yan sanda

Rundunar yan sandan kasar nan ta ce daukar doka a hannu da wasu ke yi zai jawo babban kalubale kuma cin fuska be ga doka da oda.

ACP Olumuyiwa Adejobi, shi ne jami'in hulda da jama'a na rundunar na kasa, ya ce daukar doka a hannu zai iya jawo asarar rayuka da dukiyoyin jama'a.

Ana samun karuwar daukar doka a hannu

Yan sandan Najeriya sun bayyana damuwa kan yadda ake samun mutane su na kutsawa ofishin yan sanda domin daukar doka a hannunsu.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun cafke wata dattijuwa da harsasai 350 za ta kai wa ƴan bindiga

Rundunar ta bayyana cewa akwai lokutan da jama'a suka kai hari ofishin yan sanda da ke Edo tare da kwace wani da ake zargi da ta'addanci kuka aka kashe shi.

Yan sanda sun koka kan rashin mutunta doka

A wani labarin kun ji cewa rundunar yan sandan kasar nan ta koka kan mutukan da su ke tafiya da jami'an tsaron da ke tare su a hanya domin gudanar da ayyukansu.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar, ACP Olamuyiwa Adejobi ya gargadi direbobin su daina tafiya da jami'an tsaron da ke shiga abin hawansu a hanya, domin haka ya saba doka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.