Jigawa: Adadin Wadanda Suka Mutu a Fashewar Tanka Ya Haura 175, Bayanai Sun Fito

Jigawa: Adadin Wadanda Suka Mutu a Fashewar Tanka Ya Haura 175, Bayanai Sun Fito

  • Al'ummar jihar Jigawa na ci gaba da zaman makokin mutuwar kimanin mutane 180 daga fashewar wata tankar mai a garin Majiya
  • An rahoto cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata, 15 ga watan Oktoba bayan wata tanka ta fadi a garin, inda mutane suka je dibar mai
  • Wasu 'yan garin Majiya da aka zanta da su, sun bayyana cewa mutane 104 ne suka mutu nan take yayin da wasu suka mutu a asibiti

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jigawa - An samu karuwar mutanen da suka mutu sakamakon fashewar tankar mai a ranar Talatar da ta gabata a garin Majiya na jihar Jigawa.

Wani sabon rahoto da aka samu ya nuna cewa adadin wadanda suka mutu a fashewar tankar ya kai 180 ya zuwa ranar Lahadi 20 ga Oktoba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shiga gari sun bude wuta, da dama sun mutu

Mazauna garin Majiya da ke Jigawa sun yi magana kan mutanen da suka mutu a fashewar tanka
Jigawa: Mazauna garin Majiya sun ce adadin wadanda suka mutu a fashewar tanka ya kai 180. Hoto: AMINU ABUBAKAR
Asali: Getty Images

'Mutane na cikin makoki' - Majia

Jabir Abdullahi Majiya, wani mazaunin garin ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Mutanen da suka rasa ‘yan uwansu har yanzu suna cikin bakin ciki yayin da adadin wadanda suka mutu ke ci gaba da karuwa.
"Ina aiki a makarantar 'Adams Science Tahfizul Quran', inda motar ta fado daidai kofar makarantarmu. Har yanzu mutane suna cikin makoki."

Ya kara da cewa al'ummar garin ba za su iya mantawa da fashewar tankar ba, domin kusan kowane iyali ya rasa dan uwansa.

Mutane 180 sun mutu a Jigawa

Mustapha Abdullahi Majiya ya ce iyalansa sun rasa ‘yan uwansu na jini kusan mutum 52.

Ya ce:

“Wannan lamari ne mai ban tsoro da ba mu taba fuskantar irinsa ba a wannan garin. Iyalaina sun rasa danginsu na jini kusan mutum 52.”

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya bayyana babbar matsalar Najeriya da Tinubu ya fara magancewa

Wani mazaunin garin, Adamu Lawan Majiya, ya ce zai yi wahala a samu gidan da ba su rasa wani nasu a fashewar tankar ba, inda ya ce adadin wadanda suka mutu ya kai 180.

Lawan ya ce mutane 104 ne suka mutu a wurin da fashewar ta auku, yayin da wasu kuma suka mutu bayan an kai su asibiti.

Tankar mai ta fashe a Jigawa

Tun da fari, mun ruwaito cewa wata motar dakon mai da ta tashi daga Kano zuwa Yobe, ta fadi tare da fashewa a garin Majiya, karamar hukumar Taura a jihar Jigawa.

An rahoto cewa jim kadan bayan da jama'ar garin suka fara kwasar man da ke fitowa daga motar ne wuta ta kama, inda motar ta fashe tare da halaka daruruwan mutane.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.