Cuta ba Mutuwa ba: Obasanjo Ya Fadi Ciwon da Ya Kama Shi Bai Sani ba

Cuta ba Mutuwa ba: Obasanjo Ya Fadi Ciwon da Ya Kama Shi Bai Sani ba

  • Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ya taɓa samun cutar kurumta ba tare da ya sani ba
  • Obasanjo ya bayyana cewa sai bayan da aka duba lafiyar kunnuwansa ne sannan aka gaya masa cewa yana da ciwon rashin ji na kaso 25%
  • Tsohon shugaban ƙasan ya bayyana cewa mutane da dama na ɗauke da cutar ba tare da sun sani ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi magana kan cutar da ta taɓa kama shi ba tare da ya sani ba.

Cif Olusegun Obasanjo ya ce ya taɓa samun matsalar rashin ji ta kaso 25% cikin 100% ba tare da saninsa ba.

Obasanjo ya magantu kan cutar kurumta
Obasanjo ya ce ya taba yin cutar kurumta Hoto: Phill Magakoe
Asali: Getty Images

Obasanjo ya ziyarci Bauchi

Kara karanta wannan

Obasanjo ya bayyana babban abin da ke barazana ga tsaron Najeriya

Tsohon shugaban ƙasan ya bayyana haka ne a Bauchi a ranar Lahadi a lokacin da ya kai wa Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Suleiman-Adamu ziyara, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Obasanjo, mutane da yawa a duniya suna da cutar kurumta ba tare da sun sani ba har sai sun je a duba lafiyar jinsu kafin nan a bayyana musu, rahoton The Guardian ya tabbatar.

Ya ba da labarin cewa yana ƙasar waje lokacin da wani mutum ya yi masa magana amma ba ya jinsa sosai, inda ya dage cewa babu wani abu da ke damun kunnuwansa.

Obasanjo ya taɓa samun cutar kurumta

Sannan sai mutumin ya nemi izininsa domin ya duba masa lafiyar kunnuwansa.

Obasanjo ya ce sakamakon duba lafiyar kunnuwan na sa ya nuna cewa yana da cutar kurumta ta kaso 25%.

Kara karanta wannan

'Ta dawo makabarta': Obasanjo ya fadi dalilin rashin samun cigaba a Najeriya

"Bayan da sakamakona ya fito, sai na nemi mutumin da ya duba lafiyar babban jami’in tsaro na a lokacin amma abin mamaki, ya fi ni kurumcewa."

- Olusegun Obasanjo

Obasanjo ya jawo hankalin shugabanni

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo ya ce za a samu matsala mai girma idan shugabannin Afirka ba su magance matsalolin da ke addabar matasa ba.

Cif Obasanjo ya bayyana cewa wannan fatara da talaucin da al'umma ke ciki a nahiyar Afirka ba kaddara ba ce daga Allah, wasu mutane nw suka jawo matsalolin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng