Wike Ya Sake Nuna Yatsa ga Gwamnan PDP da Suke Takun Saka
- Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike ya yi kakkausar suka ga magajinsa gwamnan jihar Rivers, Sir Siminalayi Fubara
- Wike ya caccaki gwamnan ne kan wasu kalamai da ya yi na rashin mutuntawa ga wasu manyan lauyoyi
- Ministann ya kuma gargaɗi masu son ganin an hukunta shi a jam'iyyar PDP kan su shiga taitayinsu domin shi ba kanwar lasa ba ce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Rivers - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya caccaki magajinsa kuma gwamnan jihar Rivers, Sir Siminialayi Fubara.
Wike ya caccaki Fubara ne kan wasu kalamai na rashin mutuntawa da ya yi a kwanakin baya kan wasu manyan lauyoyi.
Wike ya caccaki Fubara
Wike ya soki gwamnan ne a wajen wani taro da aka gudanar a jihar Rivers a ranar Asabar, 19 ga watan Oktoban 2024, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda gwamnan ya yi rashin kyautatawa ga wasu manyan mutane uku a jihar waɗanda suka kai ruwa rana wajen ganin an zaɓe shi ya zama gwamna.
Wike ya ɗaga yatsa ga masu adawa da shi
Wike ya kuma yi kakkausar suka ga masu son ganin an hukunta shi a jam'iyyar PDP, inda ya ce suna ginawa kansu ramin mugunta ne.
"Ba mu fara ba. Za mu iya kuma a shirye muke."
"Duba mutanen da suke magana akan dakatar da ni. Rivers kadara ce kuma ba za mu taɓa zuwa mu rusuna muku ba. Idan baku san cewa Rivers kadara ba ce, idan kun isa ku yi abin da za ku yi daga inda kuke."
- Nyesom Wike
Karanta wasu labaran kan rikicin Rivers
- Rikicin Rivers: Wike ya bayyana abin da zai kawo zaman lafiya
- Wike vs Fubara: Mutane 4 da za su iya kawo karshen rikicin siyasar jihar Rivers
- Nyesom Wike ya bayyana dalilin barkewar rikici a jihar Rivers
Wike ya caccaki Atiku
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya caccaki tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 a PDP, Atiku Abubakar.
Wike ya bayyana cewa ƴan Najeriya sun ki jinin Atiku, bayan da ya tsaya takara a zaben shugaban kasa kuma ya fadi “sau da yawa” a tarihin siyasarsa.
Asali: Legit.ng