A da N30,000 Nake Kashewa: Direba Ya Yi Tsokaci Bayan Sauya Motarsa Zuwa CNG
- Wani direban mota ya sauya motarsa daga amfani da man fetur zuwa gas din CNG, hakan ya rage masa kashe kudi
- A wata tattaunawa da aka yi dashi, ya ce a baya kullum sai ya kashe N30,000 ko sama a sayen man fetur
- Yayin da mutane suka ji ya ce yanzu N7,000 yake kashewa a rana, sun tambayi ko ya rage kudin sufuri da yake karba a hannun fasinja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Yayin da a Najeriya ake ci gaba da karbar gas din CNG saboda tsadar man fetur, direbobi sun bayyana ra’ayoyinsu.
A wata tattaunawa da iTV ta yi da direbobi, sun bayyana ra’ayoyinsu da kuma yadda suke karbar sauya motocinsu zuwa CNG.
Yadda ake karbar CNG a Najeriya
Idan baku manta ba, wani farfesa a jami’ar Najeriya ya ce ba zai taba sauya motarsa zuwa CNG ba ko ya za a yi dashi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A bangare guda, direbobin motocin haya sun fadi ra’ayinsu, kuma sun karbi CNG hannu biyu.
A cewar wani daga cikin direbobin, kudin da yake kashewa na sayen man fetur ya ragu ainun bayan komawa CNG.
A cewarsa, a madadin kashe N30,000 da yake a rana, yanzu yana kashe N7,000 ne kawai ta hanyar amfani da CNG.
An yada bidiyon hirarsa a shafin TikTok na @pcngi, duba bidiyon a kasa:
Martanin jama'a a kafar TikTok
user4170322148490:
“Ka yi amfani da albashinka na watanni takwas ta sauya. Sannan duk sadda kake bukatar gas ka tafi Lekki ko Maitama a Abuja.”
pcnginitiative:
“Ana kirkirar wuraren shan iskar CNG a kasar ko ta ina!!! Wannan ba zai zama wata matsala ba.”
smoltfrank:
“A ina ake sauyawa don Allah?”
30BGmetro:
“A ina kake a birnin Benin?”
Godwin_chukwu:
“A hankali zai tashi.”
pcnginitiative:
“CNG ya fi araha sosai...kuma ba za a daina amfani da CNG ba.”
wisdom benjamin:
“Haka zai karbi kudi daidai na abokan aikinsa masu aiki da man fetur.”
businessmencloset:
“Ina fatan dai sun rage kudin sufuri?”
holawalay (Wales):
“Kudin sufurinsa zai yi tsada saboda sauya mota zuwa CNG bai da sauki.”
Wasu direbobi sun ki karbar CNG
A wani labarin, man iskar gas na CNG yana da arha wanda hakan ya sanya zama makwafin man fetur domin yin amfani da shi a motoci.
Gwamnatin tarayya ta fito da tsarin PCNGi wanda zai mayar da hankali wajen ganin an koma amfani da CNG a kasar nan domin samun sauki.
A karkashin tsarin akwai shirin samar da wuraren da za a rika mayar da motoci masu amfani da man fetur komawa yin amfani da CNG.
Asali: Legit.ng