Zaben Ciyamomi: Halin da Ake Ciki a Kaduna kan Dokar Hana Zirga Zirga
- Mutane a birnin Kaduna sun yi biris da dokar hana zirga-zirga da gwamnatin jihar ta sanya domin zaɓen ƙananan hukumomin jihar
- Masu ababen hawa sun ci gaba da gudanar da harkokinsu duk kuwa da dokar hana zirga-zirgar da aka sanya a ranar Asabar, 19 ga watan Oktoba 2024
- Tun da farko dai gwamnatin jihar ta sanya dokar hana zirga-zirgar daga ƙarfe 6:00 na safe zuwa ƙarfe 7:00 na Yamma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Mutanen Kaduna a ranar Asabar sun bijirewa dokar hana zirga-zirga da gwamnatin jihar ta sanya.
Gwamnatin jihar ta sanya dokar hana zirga-zirgar ne domin zaɓen ƙananan hukumomin jihar na ranar Asabar, 19 ga watan Oktoban 2024.
An yi biris da dokar hana zirga-zirga a Kaduna
Jaridar Daily Trust ta ce sai dai duk da dokar, masu ababen hawa musamman masu Keke NAPEP da ƴan Achaɓa sun ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum a kan manyan tituna irin su Ahmadu Bello Way da Ali Akilu Way.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An dai sanya dokar hana zirga-zirgar ne daga ƙarfe 6:00 na safe zuwa ƙarfe 7:00 na Yamma.
Jami’an tsaron da aka girke a kan hanyar Ali Akilu da ke cikin birnin Kaduna suna gudanar da aikin bincike, duk da cewa ba su kama wani da ya keta doka ba.
Mutane sun ci gaba da harkokinsu a Kaduna
An kuma lura da cewa wasu garejin kanikanci sun kasance a buɗe domin gudanar da ayyukansu a wasu unguwannin duk da dokar hana zirga-zirgar.
Wani mazaunin birnin mai suna Adamu Hassan wanda ya ziyarci Kasuwar Mogadishu Layout ya bayyana cewa masu sayar da abinci sun fito wajen kasuwancinsu.
"Wasu ƴan kasuwa sun buɗe shagunansu saboda yanzu na sayi gari a Kasuwa. Na ga wasu mata suna ta harkokinsu."
- Adamu Hassan
Gwamnatin Kaduna ta musanta ciyo bashi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa tun kafuwar gwamnati mai ci a ƙarƙashin Gwamna Uba Sani ba ta karɓo wani sabon bashi ba.
Gwamnatin ta yi watsi da rahotannin da ke cewa ta ciyo bashin Naira biliyan 36 a cikin watanni shida da suka gabata, inda ta bayyana rahoton a matsayin ƙarya da yaudara.
Asali: Legit.ng