Sarki Sanusi II Ya Nada Kawun Gwamna Abba Kabir Yusuf Babban Matsayi a Masarautar Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya halarci taron nadin sarauta a fadar Mai Martaba Muhammadu Sanusi II
- An nada kawun gwamna a matsayin Danmakwayon Kano, Abba ya yaba wa sarkin Kano na yanzu
- Jihar Kano na daga cikin jihohin da Arewacin Najeriya ke alfahari da su, musamman ta fuskar masarauta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Kano - An nada kawun gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a matsayin Danmakwayon Kano a fadar Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II.
Sabon Danmakwayon Kano na yanzu shi ne Alhaji Abba Yusuf, wanda ya kasance kawun gwamna mai ci a jihar ta Kano.
Baya ga wannan, an kuma nada wasu sabbin hakimai guda shida na yankuna a jihar mai dogon tarihi.
Nadin sarautar da aka yi a Kano
Da yake bayyana nadin da kuma halartar bikin nadin sarautar, gwamna Abba ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Na samu karamci a fadar Sarkin Kano na halartar bikin nadin sarautar hakimai guda shida, ciki har da kawuna, Alhaji Abba Yusuf a matsayin Danmakwayon Kano, sarautar da mahaifinsa da ya rasu ya rike.”
Abba ya yiwa Sarki Sanusi godiya
A bangare guda, gwamnan ya yiwa Sarkin Kano fatan alheri tare da bayyana amincin da aka samu a masarautar.
A cewarsa:
“Dole ne in yaba wa Mai Martaba, Khalifa Muhammadu Sanusi II, Sarkin Kano bisa tabbatar da daidaito a masarautar mai martaba.”
Allah ya dafawa sarakunan gargajiya, gwamna Abba
Daga karshe, gwamnan ya yiwa dukkan sarakunan gargajiya a jihar da kewaye fatan alheri, inda ya yi masu addu’ar Allah ya dafa masu.
“Allah Madaukakin Sarki Ya yi wa dukkan Sarakunan gargajiya na Kano jagora.”
Jihar Kano na daga cikin jihohin Arewacin Najeriya da ke dimbin tarihi, musamman a fannin sarauta da kasuwanci.
Kalli hotunan da Abba ya yada:
Gwamna Abba ya yi kora a Kano Pillars
A wani labarin, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu kan korar shugabannin rikon kwarya na kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars.
Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar, Shehu Wada Sagagi ne ya tabbatar da hakan a wata hira da manema labarai a jihar Kano.
A shekarun baya Kano Pillars na ɗaya daga cikin kungiyoyin da tauraruwarsu ke haskawa a gasar cin kofin firimiya na gida Najeriya, Leadership ta ruwaito.
Asali: Legit.ng