An Shiga Duhu: Wutar Lantarkin Najeriya Ta Sake Rikicewa a Karo Na Uku Cikin Mako Guda
- Tsarin wutar lantarkin Najeriya ya sake birkicewa a karo na uku, inda 'yan Najeriya ke kukan duhu
- A cikin mako guda, an samu daukewar wutar lantarki mai tsanani, inda 'yan Najeriya ke fuskantar asarar dukiya
- Mai sana'ar fawa, Muhammad Adamu ya bayyanawa Legit irin asarar nama da ya yi a ranakun Litinin da Talata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Najeriya - A karo na uku cikin mako guda, tsarin wutar lantarkin Najeriya ya sake birkicewa a ranar Asabar 19 ga watan Oktoba.
An daina samar da wutar lantarki a kasar tun da sanyin safiyar Asabar kusan karfe 8:16, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Idan baku manta ba, a baya myn ruwaito cewa wutar lantarkin Najeriya ta dauke dif a ranakun Litinin da Talata.
Yadda matsalar take a wannan karon
Binciken jaridar Punch ya tabbatar da cewa an samar da megawatt 3,042 na wuta da misalin karfe 8 na safe, sannan ya kai kololuwar megawatt 3,968 da misalin karfe 7 na safe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai, samar da wutar ya ragu zuwa megawatt 47 da misalin karfe 9 na safe, wanda ya nuna samuwar matsala ga tsarin wutar.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, isowar wuta ga kamfanonin rarraba wutar lantarki ya tsaya a megawatt 0.00.
Ba a samu tabbacin musabbabin cabewar tsarin ba a ya zuwa yanzu, domin ba a samu damar tattaunawa da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya ba.
Na yi asarar kusan rabin saniya
Wani mahauci da ke zaune a unguwar Bye Pass da ke Gombe, ya fadi irin asarar da ya yi bayan daukewar wuta.
A cewar Muhammad Adamu:
"Daukewar wutan nan ya taba ni, domin na dogara da ita don amfani da na'urar daskarar da abinci, amma ba a kawo ta ba.
"Haka na yi asarar kusan rabin saniya saboda na saka a na'urar da jiran za a kawo wuta, da ba a kawo ba kaya ya rube, haka na tattara na sayar, ban mayar da kudin ba."
Yadda ta kaya a makon jiya
A wani labarin, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa dole a cigaba da samun matsalar wutar lantarki a fadin kasar nan, saboda wasu dalilai.
Ministan makamashin ya ce amma akwai hanyar da za a bi wajen magance matsalar yawaitar lalacewar turakun lantarki.
Ya zama ruwan dare a samu daukewar wutar lantarki a Najeriya, kuma hakan yana shafan kasuwancin 'yan kasar.
Asali: Legit.ng