Gwamna Fubara Ya Amince da N85,000 a Matsayin Mafi Karancin Albashi a Ribas

Gwamna Fubara Ya Amince da N85,000 a Matsayin Mafi Karancin Albashi a Ribas

  • Gwamna Siminalayi Fubara ya kere N70,000, ya amince da N85,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi a jihar Ribas
  • Shugaban ma'aikatan jihar, George Nwaeke ya ce gwamnan ya amince da sabon albashin ne yayin ganawa da ƴan kwadago
  • Fubara ya zama gwamna na biyu bayan Babajide Sanwo-Olu da ya kai albashi N85,000, sama da na gwamnatin tarayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara ya amince da N85,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata a jihar Ribas.

Shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Ribas, George Nwaeke, shi ne ya sanar da haka yau Jumua'a, 18 ga watan Oktoba, 2024.

Gwamna Siminalayi Fubara.
Gwamna Fubara ya amince da N85,000 a matsayin mafi karancin albashi a Ribas Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Ya ce Fubara ya amince da sabon albashin ne yayin wata ganawar sirri da ƴan kwadago da wasu manyan kusoshin gwamnati a Fatakwal, rahoton Channels tv.

Kara karanta wannan

"Kuna da damar taimakon ƴan Najeriya," Jigon APC ya dura kan Kwankwaso da Atiku

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan taron ne Nwaeke ya tabbatar da cewa sabon albashin N85,000 da mai girma gwamna ya amince da shi za a fara aiwatar da shi nan take.

Ƴan kwadago sun yabawa gwamna Fubara

A nasa ɓangaren, shugaban tawagar wakilan ƴan kwadago da suka halarci zaman, Chukwu Emecheta ya yabawa Gwamna Fubara.

Ya ce gwamnan ya cancanci a yaba masa bisa wannan karin albashi da ya yi wanda ya yi daidai da buƙatun ma'aikatan jihar Ribas.

Haka nan kuma Emecheta ya nuna matukar jin daɗinsa bisa yadda gwamnan ya ɗauki ma'aikata da muhimmanci, Leadership ta kawo.

NLC ta ce ma'aikata za su samu sauki

Bugu da ƙari, da yake nasa jawabin, shugaban ƙungiyar kwadago watau NLC ta reshen Ribas, Alex Agwanwor ya ce sabon albashin zai ragewa ma'aikata raɗaɗi.

Ya ƙara da cewa mafi karancin albashin da gwamnan ya amince da shi zai taimaka matuka wajen rage wahalhalu da matsin da ma’aikata ke fuskanta a jihar.

Kara karanta wannan

"Allah ji ƙansu," Gwamnan Abba ya yi maganar mutuwar sama da mutum 100 a Jigawa

Gwamnan Legas ya amince da sabon albashi

A wani rahoton kuma gwamnan jihar Legas ya yi alƙawarin biyan ma'aikata N85,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi nan ba da daɗewa ba.

Mai girma Babajide Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi ranar Laraba, 16 ga watan Oktoba, 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262