Gowon @90: Buhari Ya Yi Yabo da Tsohon Shugaban Kasa Ya Kara Shekara a Duniya

Gowon @90: Buhari Ya Yi Yabo da Tsohon Shugaban Kasa Ya Kara Shekara a Duniya

  • Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya mika sakon fatan alheri ga takwaransa na mulkin soja kuma mai gida
  • Muhammadu Buhari ya taya tsohon shugaba Janar Yakubu Gowon mai ritaya murnar cika shekaru 90 da haihuwa a yau
  • Ya bayyana cewa yan kasar nan ba za su taba mantawa da gudunmawar da Yakubu Gowon ya bayar wajen cigaba ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina - Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yabi kyawawan manufofin da tsohon shugaban mulkin Soja, Janar Yakubu Gowon ke da su ga kasar nan.

Tsohon shugaban ya fadi haka ne a sakon taya murnar zagayowar ranar haihuwa yayin da Janar Yakubu Gowon mai ritaya ya cika shekaru 90 a duniya.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya caccaki yadda Tinubu, Shettima su ka bar Najeriya da matsala

Gowon
Buhari ya taya tsohon shugaba Gowon murnar cika shekaru 90 Hoto: @GarShehu
Asali: Twitter

A sakon da mai magana da yawun tsohon shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar, ya ce Yakubu Gowon na son a samu hadin kai a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhammadu Buhari yake cewa burin Gowon a zama tsintsiya madaurinki daya.

Buhari ya fadi halin kirkin Yakubu Gowon

Jaridar The Nation ta wallafa cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yabi halayen kwarai da kyawawan manufofin Janar Gowon ga kasa.

Ya kara da cewa yan Najeriya ba za su manta da jagoranci na gari da Janar Gowon ya yi a lokacin da ya ke mulkin kasar nan ba.

Ya kara yabawa Janar Gowon mai ritaya kan yadda har yanzu ba ya gajiyawa wajen ba kasar nan shawarwari na gari.

"Mu na alfahari da kai:" Buhari ga Gowon

Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana yadda yan kasar nan ke matukar alfahari da takwaransa na mulkin sojan.

Kara karanta wannan

'Yana yawo cikin dare,' Sanata ya tona yadda Tinubu yake zagaya gari a boye

Muhammadu Buhari ya yabi yadda tsohon shugaba Gowon ya ja tawagar dakarun kasar nan wajen tabbatar da kare martabar Najeriya a baya.

Hadimin Buhari ya gano matsala a gwamnati

A baya mun ruwaito cewa tsohon hadimin Yemi Osinbajo, ya ce akwai alamun rashin jituwa tsakanin shugaban kasa, Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima.

Tsohon hadimin mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande ya bayyana cewa idan babu burbushin matsala a tsakanin jagororin, bai dace dukkaninsu su bar kasar ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.