Jonathan Ya Caccaki Bangaren Shari'a, Ya Hango Kuskuren da Suke Yi

Jonathan Ya Caccaki Bangaren Shari'a, Ya Hango Kuskuren da Suke Yi

  • Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan ya nuna damuwarsa kan wadu hukunce-hukuncen da ɓangaren shari'a ke yankewa
  • Jonathan ya bayyana cewa wasu daga cikin hukunce-hukuncen da suka shafi al'amuran siyasa ko kaɗan babu adalci a ciki
  • Ya nuna damuwarsa kan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke wanda ya ba da dama ga shugaban jam'iyya a matakin mazaɓa ya dakatar da shugaban jam'iyya na ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Goodluck Jonathan ya caccaki ɓangaren shari’a.

Shugaba Goodluck Jonathan ya caccaki ɓangaren shari'ar ne kan wasu hukunce-hukuncen da kotuna daban-daban suka yanke a ƴan kwanakin nan.

Jonathan ya soki bangaren shari'a
Jonathan ya caccaki bangaren shari'a Hoto: Goodluck Jonathan
Asali: Facebook

Shugaba Jonathan ya bayyana hakan ne ya yin da yake magana a wajen bikin cika shekaru 67 na babban lauya, Farfesa Mike Ozekhome, SAN, a birnin tarayya Abuja, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Zababben gwamna ya bankado badakalar da ake shiryawa kafin a mika masa mulki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jonathan ya caccaki ɓangaren shari'a

Jonathan ya ce ya damu da yadda al’amura ke tafiya a ƙasar nan, musamman dangane da yanke hukunci kan shari’o’in da suka danganci siyasa. 

Ya ce wani hukunci da ya ɗaure masa kai shi ne hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke na cewa shugaban jam’iyya a matakin mazaɓa zai iya dakatar da shugaban jam’iyya na ƙasa. 

A cewarsa, ba wa shugabannin jam'iyya a matakin mazaɓa damar dakatar da shugabanninsu na ƙasa saɓawa ƙa’idar adalci ne.

"Ba zai yiwu a gaya min cewa shugaban tsangaya zai iya korar shugaban jami'a ba."
"Tun da aka yanke wannan hukunci, ya haifar da ruɗani. A yanzu PDP tana cikin rikici saboda wannan hukuncin. Ita ma APC ta fuskanci irin wannan matsala a wani lokaci."

- Goodluck Ebele Jonathan

Jonathan ya ƙarfafa gwiwar ƴan Najeriya

Kara karanta wannan

Jagororin APC sun ba 'yan Najeriya shawara kan gwamnatin Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ya ƙarfafi yan ƙasar nan a dai-dai lokacin da aka cika shekaru 64 da samun yanci.

Tsohon shugaban ya ce duk da halin da ake ciki mai dimbin kalubale, bai kamata a karaya da gina kasa cike da arziki da kwanciyar hankali ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng