Fashewar Tankar Mai: Ganduje Ya Yi Alhini kan Asarar Rayukan da Aka Yi a Jigawa
- Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya nuna alhininsa kan iftila'in fashewar tankar maibda ya auku a Jigawa
- Ganduje ya yi wa gwamnati da al'ummar jihar Jigawa ta'aziyya kan rasuwar mutanen da aka samu sakamakon fashewar tankar man
- Shugaban na APC ya yi wa addu'ar Allah Ya ji ƙan waɗanda suka rasu Ya kuma ba iyalansu haƙuri da juriyar rashin da suka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Jigawa game da fashewar tankar man da ya auku.
Fashewar tankar man dai ya yi sanadiyyar rasuwar mutane kusan 150 yayin da wasu da dama suka jikkata.
Ganduje ya yi ta'aziyyar rasuwar ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, 17 ga watan Oktoban 2024, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganduje ya yi ta'aziyyar gobarar Jigawa
Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar jihar Jigawa, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.
Ya nuna alhininsa game da mummunan fashewar tankar man da ya auku a garin Majia da ƙe karamar hukumar Taura, inda aka rasa rayukan mutane masu yawa.
Ya kuma yi ta’aziyya ga waɗanda abin ya shafa, iyalansu, da ɗaukacin al’ummar jihar Jigawa.
"Na yi matuƙar bakin ciki da samun labarin fashewar wata tankar mai da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 150 tare da jikkata wasu da dama."
"Ina addu'ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya jiƙan waɗanda suka rasu Ya kuma ba iyalansu haƙurin jure wannan rashin."
- Abdullahi Umar Ganduje
Remi Tinubu ta yi ta'aziyya ga gwamnatin Jigawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu ta miƙa saƙon ta’aziyya ga gwamnan Jigawa, Mallam Umar Namadi, kan fashewar tankar man fetur.
Sanata Oluremi Tinubu ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici, inda ta yi addu’ar Allah ba iyalan mamatan ikon jure rashinsu.
Asali: Legit.ng