CNG: Ana Jimamin Hatsarin Jigawa, Mota Mai Amfani da Gas Ta Fashe a Gidan Mai

CNG: Ana Jimamin Hatsarin Jigawa, Mota Mai Amfani da Gas Ta Fashe a Gidan Mai

  • Wata mota da ke amfani da iskar gas na CNG ta gamu da hatsari a wani gidan mai da ke birnin Benin na jihar Edo a Najeriya
  • Wani faifan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda motar ta yi raga-raga bayan aukuwar fashewar a yau
  • Ba a samu asarar rai ba sakamakon lamarin amma rahotanni sun nuna cewa mutane uku sun samu raunuka daban-daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - An shiga jimami a Edo bayan wata mota ta fashe a wani gidan mai a birnin Benin na jihar.

Motar da ke amfani da iskar gas na CNG ta fashe ne a gidan man NIPCO dake Aduwawa kan babbar hanyar Benin zuwa Auchi a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

"Allah ji ƙansu," Gwamnan Abba ya yi maganar mutuwar sama da mutum 100 a Jigawa

Mota mai amfani da CNG ta fashe a Edo
Mota mai amfani da iskar gas na CNG ta fashe a Edo Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Mota mai amfani da CNG ta fashe

Jaridar Vanguard ta ce a wani faifan bidiyo da aka yi ta yaɗawa a shafukan sada zumunta, an nuna yadda motar ta yi raga-raga bayan aukuwar fashewar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutanen da ke kusa da wurin sun yi ta gudu domin tsira da rayukansu yayin da ƙarar fashewar ta haifar da firgici a tsakanin mazauna yankin.

Jaridar Leadership ta ce mutane uku sun samu raunuka daban-daban kuma an garzaya da su wani asibiti mai zaman kansa domin kula da lafiyarsu.

Ana fargabar mayar da motoci amfani da CNG

Fashewar dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake nuna fargaba kan mayar da motoci masu amfani da man fetur zuwa amfani da iskar gas na CNG.

Gwamnatin tarayya dai tana tallata tsarin mayar da motoci zuwa masu amfani da iskar gas na CNG domin rage tsadar sufuri bayan cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Bayan rasa rayuka a Jigawa, barci ya dauke direba, wata tankar fetur ta kama da wuta

Karanta wasu labaran kan haɗuran mota

Tankar mai ta fashe a Jigawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa kusan mutane 100 ne suka bar duniya sakamakon faɗuwar da wata tankar mai ta yi a jihar Jigawa.

Faduwar tankar man wanda ya auku a ƙauyen Majiya da ke ƙaramar hukumar Taura ya kuma yi sanadiyyar raunata mutane sama da 50.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng