Zababben Gwamna Ya Bankado Badakalar da Ake Shiryawa Kafin a Mika Masa Mulki

Zababben Gwamna Ya Bankado Badakalar da Ake Shiryawa Kafin a Mika Masa Mulki

  • Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya koka kan yadda aka shirya maƙarƙashiya kafin a miƙa masa mulki
  • Okpebholo ya zargi gwamna Godwin Obaseki da ci gaba da ciyo basussuka daga wajen bankuna ta hanyar da ba ta dace ba
  • Ya nuna damuwarsa kan yadda jami'ai ke wawushe dukiya da kadarori yayin da ya rage saura ƙasa da wata ɗaya su bar mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Zaɓaɓɓen gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya yi kira ga bankuna da su dakatar da ba gwamnatin jihar bashi a lokacin da ake shirin miƙa mulki.

Monday Okpebholo ya kuma nuna damuwarsa kan yadda jami’an gwamnatin Mai girma Godwin Obaseki ke wawushe kuɗi da kadarorin gwamnati.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu da ƴan ƙwadago sun cimma matsaya kan farashin kayan abinci

Zababben gwamnan Edo ya mika korafi wajen EFCC
Monday Okpebholo ya zargi gwamnatin Obaseki da karbo basussuka Hoto: Sen. Monday Okpebholo
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Godswill Inegbealso, ya fitar, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane zargi zaɓaɓɓen gwamnan ya yi?

Zaɓaɓɓen gwamnan ya kuma buƙaci hukumomin EFCC da DSS da su gudanar da bincike kan lamarin.

Ya ƙara da cewa ko kaɗan wannan ba abin da za su lamunta ba ne, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

"Abin takaici ne ana saura ƙasa da wata ɗaya a miƙa mulki, gwamnati mai barin gado ta Gwamna Godwin Obaseki, na ci gaba da karɓo basussuka daga bankuna ta hanyar da ba ta dace ba."
"Muna kuma sane da yadda ake sata da lalata kadarori da suka haɗa da ababen hawa, kayan ɗaki, na'urori daga ofisoshi da gidajen gwamnatin jihar Edo."
"Dangane da haka, muna kira ga hukumomin da abin ya shafa, da suka haɗa da EFCC, ƴan sanda, DSS, da su binciki wannan zargin, tare da tabbatar da hukunta waɗanda aka samu da laifi."

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya saukakawa talaka, ya fara siyar da kayan abinci masu rahusa

- Godswill Inegbealso

Ɗan takarar gwamna ya ɗauki dangana

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar jam'iyyar LP a zaɓen gwamnan jihar Edo, Olumide Akpata, ya ɗauki mataki bayan ya sha kaye a zaben da ya gabata.

Akpata ya ce ba zai je kotu ba duk da cewa an tafka kura-kurai a zaben na Edo wajen sayen kuri’u da saba dokar tattara sakamakon zaben da ba a taba ganin irinsa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng