Gwamna da Wasu Manyan Mutane Sun Yi Jimami da Allah Ya Yi wa Sarki a Arewa Rasuwa

Gwamna da Wasu Manyan Mutane Sun Yi Jimami da Allah Ya Yi wa Sarki a Arewa Rasuwa

  • Gwamnan Kwara, sarkin Ilorin da kakakin majalisar dokoki sun yi ta'aziyyar rasuwar sarkin Gobir na masarautar Ilorin
  • Allah ya karɓi rayuwar basaraken kuma shugaban kwalejin sufurin jiragen sama ta Ilorin, Muhammad Yusuf Gobir yana shekara 62
  • Gwamna AbdulRazaq ya tabbatar da wannan rashi a wata sanarwa da sakataren yaɗa labaransa, Rafiu Ajakaye ya fitar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kwara - Allah ya yi wa Sarkin Gobir na masarautar Ilorin a jihar Kwara, Muhammad Yusuf Gobir rasuwa yana da shekara 62.

Manyan mutane a jihar Kwara da suka haɗa da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq sun yi ta'aziyyar wannan rashin tare da karrama marigayin.

Gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq.
Gwamnan Kwara da wasu manyan mutane sun yi alhirin rasuwar sarkin Gobir na masarautar Ilorin Hoto: AbdulRahman AbdulRazaq
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta ce sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu Gambari da kakakin majalisar dokokin jihar Kwara na cikin manyan mutanen da suka yi ta'aziyya.

Kara karanta wannan

Fashewar tankar mai: Ganduje ya yi alhini kan asarar rayukan da aka yi a Jigawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Kwara ya tabbatar da rasuwar Sarkin Gobir

A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan Kwara, Rafiu Ajakaye ya fitar, Gwamna Abdulrazak ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin da nasarautar Ilorin.

Sanarwar ta ce:

"Muna sanar da rasuwar shugaban kwalejin sufurin jiragen sama ta Ilorin kuma Sarkin Gobir na masarautar Ilorin, Kyaftin Muhammad Ahmad Yusuf-Gobir.
"Muna miƙa sakon ta'aziyya ga al'ummar masarautar Ilorin musamman iyalan marigayin bisa wannan babban rashi.
"Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya yi ji rasuwar shugaban kwalejin wanda abokinsa ne na yarinta kuma ya ɗauki rashin tamkar shi aka yi wa."

Sarkin Ilorin ya yi ta'aziyyar rashin

Mai Martaba Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, a wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawunasa ya bayyana mamacin a matsayin mai tawali'u kuma basaraken mai ladabi.

Sarkin ya jajanta wa al’ummar masarautar Ilorin da iyalan marigayin, gwamnati da ɗaukacin jama’ar jihar Kwara bisa rasuwar sarkin Gobir.

Kara karanta wannan

Jami'an hukumar Hisbah a Kano za su warwasa, an gabatar da kudiri a Majalisa

Kakakin majalisar Kwara ya aika saƙo

A nasa bangaren, kakakin majalisar dokokin Kwara, Engr. Yakubu Danladi Salihu ya mika ta’aziyyarsa ga sarkin Ilorin, Gwamna AbdulRazaq da iyalan margayin.

Yakubu ya bayyana rasuwar sarkin Gobir na Ilorin a matsayin babban rashi, ba wai ga masarautar Ilorin, gwamna da iyalan Gobir kadai ba har ma da daukacin mutanen Kwara.

Ambaliya: Gwamnatin Kwara ta gargaɗi jama'a

Kun ji cewa an samu rahoton afkuwar ambaliyar ruwa a wasu yankunan Kwara yayin da aka kwashe kusan kwanaki biyar ana zabga ruwan sama.

Gwamnatin Kwara ta aika sakon gaggawa ga al'ummar jihar da ke zaune a yankunan tekuna da su koma kan tudu domin kare rayukansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262