Gwamnatin Tinubu za Ta yi Bincike kan Mutuwar Mutane Sama da 100 a Jigawa

Gwamnatin Tinubu za Ta yi Bincike kan Mutuwar Mutane Sama da 100 a Jigawa

  • Gwamnatin tarayya ta nuna damuwa kan mummunan hadarin motar mai da ya laƙume rayuka da dama a jihar Jigawa
  • Ministan fetur ya bayyana cewa ba za a bar abin ya tafi a banza ba, za a binciko sababin faruwar mummunan haɗarin
  • A yanzu haka dai mutane sama da 100 sun rasu yayin da ake cigaba da lura da wadanda suka samu raunuka a asibiti

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa - Gwamnatin tarayya ta nuna damuwa kan haɗarin motar mai da ya auku a jihar Jigawa.

Yan sanda sun tabbatar da hadarin ya jawo asarar rayuka da dukiya, mutane sama da 100 suka rigamu gidan gaskiya.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta kadu da faduwar tankar fetur a Jigawa, an fadi matakin da za a dauka

Hadarin mota
Za a yi bincike kan hadarin tankar mai a Jigawa. Hoto: @Nigerianstories
Asali: Twitter

Punch ta wallafa cewa karamin ministan man fetur ya bayyana cewa dole sai an gano dalilin faruwar hadarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a yi bincike kan hadarin Jigawa

Karamin ministan na man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri ya ba da umarnin bincike domin gano dalilin hadarin tankar mai a Jigawa.

Ministan ya bukaci a fara bincike da gaggawa kan tabbatar da abin da ya jawo hadarin domin daukar mataki.

Ministan fetur ya yi jaje a Jigawa

Jaridar Tribune ta wallafa cewa Sanata Heineken Lokpobiri ya ce ma'aikatar man fetur ta kasa tana taya iyalan wadanda suka rasu jaje.

Ya ce a madadin gwamnatin tarayya, yana yin fatan samun sauki ga waɗanda suka samu raunuka suke kwance a asibiti.

Minista fetur ya gargaɗi yan Najeriya

Ma'aikatar man fetur ta ce za ta cigaba da ƙoƙarin tabbatar da tsaron rayukan yan kasa a kan abin da ya shafi fetur.

Kara karanta wannan

'Kamar ana yakin basasa,' Tsohon minista ya gargaɗi Tinubu, yana fargabar kaurewar rikici

A karkashin haka, Lokpobiri ya bukaci yan Najeriya da su rika taka-tsan-tsan idan aka samu hadarin tankar mai.

An kori yan sanda a jihar Kwara

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sanda ta kori wasu jami'anta guda uku bisa samunsu da laifin kisan kai.

Rundunar yan sandan jihar Kwara ta bayyana cewa an samu jami'an da hannu kan kisan wani dalibi a lokacin zanga zangar tsadar rayuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng