Fashewar Tanka a Jigawa: Uwargidan Gidan Tinubu Ta Yi Ta'aziyya Mai Ratsa Zuciya

Fashewar Tanka a Jigawa: Uwargidan Gidan Tinubu Ta Yi Ta'aziyya Mai Ratsa Zuciya

  • Uwargidan shugaban ƙasar Najeriya, Remi Tinubu ta nuna alhininta kan fashewar tankar man fetur a jihar Jigawa
  • Remi Tinubu ta yi wa gwamna da al'ummar jihar ta'aziyya kan rasuwar mutanen da aka samu sakamakon aukuwar lamarin
  • Ta yi addu'ar Allah Ya jiƙansu da rahama Ya kuma ba iyalansu haƙurin jure raɗaɗin wannan rashin da suka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu ta miƙa saƙon ta’aziyya ga gwamnan Jigawa, Mallam Umar Namadi, kan fashewar da tankar man fetur da ya auku a jihar.

Fashewar tankar man wanda ya auku a daren ranar Talata ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 100 a ƙauyen Majiya da ke ƙaramar hukumar Taura ta jihar.

Kara karanta wannan

Mutane kusan 100 sun rasu sakamakon fashewar tankar mai a Jigawa

Remi Tinubu ta yi ta'aziyyar rasuwar mutane a Jigawa
Remi Tinubu ta yi wa gwamnan Jigawa ta'aziyya Hoto: Sen. Oluremi Tinubu
Asali: Facebook

Remi Tinubu ta yi ta'aziyyar ne a cikin saƙon da ta rabawa ƴan jarida a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Remi Tinubu ta yi ta'aziyyar gobarar Jigawa

Sanata Oluremi Tinubu ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici, inda ta yi addu’ar Allah Ya ba iyalan mamatan ikon jure rashinsu.

Ta kuma yi addu'ar samun sauƙi ga wadanda suka jikkata tare da fatan Allah Ya ji ƙan waɗanda suka rasu, rahoton Daily Post ya tabbatar.

"Ina jajantawa gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi, da al’ummar jihar bisa aukuwar fashewar tankar man fetur a ranar Talata, 15 ga watan Oktoba, 2024."
"Ina roƙon Allah Ya ba abokai, iyalai, da ƴan uwan waɗanda da suka rasu ikon jure wannan rashi mai raɗaɗi, ya kuma warkar da waɗanda suka jikkata."

Kara karanta wannan

Jagororin APC sun ba 'yan Najeriya shawara kan gwamnatin Tinubu

"Ina roƙon Allah Ya sa Aljannah ta zama makoma ga waɗanda suka rasu, ya kuma ba da ikon juriya ga duk mutanen da lamarin ya shafa."

- Remi Tinubu

Sanata Remi Tinubu ta ba da tallafin ambaliya

A wani labarin kuma, kun ji cewa uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta nuna alhininta kan ambaliyar ruwan da ta auku a Borno.

Sanata Remi Tinubu ta ba da gudunmawar N500m domin tallafawa mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa a jihar Borno.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng