‘Kamar Ana Yakin Basasa,’ Tsohon Minista Ya Gargaɗi Tinubu, Yana Fargabar Kaurewar Rikici

‘Kamar Ana Yakin Basasa,’ Tsohon Minista Ya Gargaɗi Tinubu, Yana Fargabar Kaurewar Rikici

  • Masana da shugabanni na cigaba da gargadin gwamnatin tarayya kan halin wahalar rayuwa da talakawa ke ciki a fadin Najeriya
  • Tsohon ministan tarayya, Cif Nduesse Essien ya ce tun da ake a Najeriya ba a taba shiga kunci da wahalar rayuwa irin na yanzu ba
  • A karkashin haka, Nduesse Essien ya yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu kan samar da sauki tun kafin rikici ya barke a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon ministan tarayya, Cif Nduesse Essien ya gargadi shugaba Bola Ahmed Tinubu kan kuncin rayuwa

Tsohon ministan tarayyar ya ce akwai hadari kan yadda Najeriya za ta kasance idan aka kure talakawan kasar.

Kara karanta wannan

Matsin rayuwa: Gwamnati za ta turawa talakawan Najeriya kudi ta asusun banki

Bola Tinubu
Tsohon minista ya gargadi Tinubu kan yunwa. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Cif Nduesse Essien ya yi jawabin ne a birnin tarayya Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon minista ya gardadi Bola Tinubu

Tsohon ministan gidaje, Cif Nduesse Essien ya ce akwai hadari mai girma kan inda Najeriya ta dosa a halin yanzu.

Cif Essien ya bukaci Bola Tinubu ya sake tunani a kan tsare-tsarensa da suka jawo wahalar rayuwa a halin yanzu.

"Najeriya ta zama kamar lokacin yakin basasa"

Tsohon ministan ya bayyana cewa tsare tsaren Tinubu sun kara jefa al'umma cikin mummunan talauci da ba taba gani ba.

Essien ya ce idan za a kwatanta wahalar da ake sha a Najeriya, za a ce ta yi kama da lokacin yakin basasa.

Tsohon minista ya bukaci a canja tsare tsare

Tsohon 'dan siyasar ya ce akwai bukatar Bola Tinubu ya canza tsare tsarensa domin kawo saukin rayuwa ga al'ummar kasar.

Kara karanta wannan

Babbar kotu ta hana EFCC kama tsohon ministan Obasanjo

Ya yi gargadin cewa ba zai yiwu a cigaba da tafiya a makance ba ta inda babu wata alama ko matakin kawo sauki ga talakawa.

Daily Post ta wallafa cewa Cif Essien ya ce idan aka cigaba a haka, talakawa za su gaza hukuri kuma abin ba zai yi kyau ga kowa ba.

Majalisa ta yi gargaɗi ga Bola Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar wakilai ta ba Bola Tinubu umarnin gaggawa wajen gabatar da kasafin kudin shekarar 2025 mai zuwa.

Yan majalisar wakilai sun yi barazanar kin karɓar kasafin kudin idan Bola Tinubu ya yi jinkirin gabatar da shi a wannan shekarar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng