Gwamnati Ta Bugi Kirji kan Ilimi, NELFUND Ta Rabawa Ɗalibai 40,000 Lamunin N10bn
- Akalla daliban kasar nan 40,000 su ka ci moriyar tallafin karatun NELFUND da gwamnatin Bola Tinubu ta kirkiro domin tallafa masu
- Wannan adadi na daga cikin dalibai 280,000 ne da su ka nemi tallafin ta shafin yanar gizo da gwamnati ta samar a shekarar 2024
- Shugaban NELFUND, Akintunde Sawyer ya tabbatar da cewa daliban da su ka ci gajiyar shirin sun fito daga makarantu daban daban
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa daliban kasar nan su na cin moriyar lamunin karatu da aka bijiro da shi domin inganta ilimi.
Shugaban hukumar kula da asusun bayar da lamunin karatu ta kasa (NELFUND) Akintunde Sawyer ne ya sanar da haka.
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa Akintunde Sawyer ya ce tuni dubunnan dalibai daga jami'o'in kasar nan sun su ka karbi lamuninsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gano nawa aka kashe a NELFUND
Shugaban asusun NELFUND, Mista Akintunde Sawyer ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta raba Naira biliyan 10 domin rabawa da daliban kasar nan.
Channels Television ta ruwaito cewa shugaban ya kara da cewa dalibai 40,000 daga manyan makarantun kasar nan daban-daban ne su ka amfana da tallafin zuwa yanzu.
Dubban dalibai sun nemi tallafin NELFUND
Shugaban hukumar asusun bayar da lamuni, Akintunde Sawyer ya ce dalibai akalla 370,000 ne su ka yi rajitsar tallafin NELFUND.
A cewar shugaban, dalibai 280,000 ne kawai su ka nemi a ba su tallafin ta hanyar shafinsa na intanet da aka kirkira domin a nemi lamunin.
Dalibai za su iya neman lamunin NELFUND
A baya kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana cewa dukkanin daliban manyan jihohin kasar nan za su iya samun lamunin karatu ta asusun NELFUND da aka bude dominsu.
Shugaban hukumar, Akintunde Sawyer ne ya bayyana haka, ya kara da cewa baya ga jami'o'in, manyan makarantun kasar nan za su iya cin moriyar tallafin idan sun nema.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng