Gwamnan Arewa Ya Saukakawa Talaka, Ya Fara Sayar da Kayan Abinci Masu Rahusa

Gwamnan Arewa Ya Saukakawa Talaka, Ya Fara Sayar da Kayan Abinci Masu Rahusa

  • Gwamnatin jihar Sokoto za ta ƙaddamar da shirin sayar da shinkafa da sauran kayan abinci a kan farashi mai rahusa
  • Gwamnatin za ta siyar da kayan abincin ne waɗanda aka zaftare kaso 55% daga farashin da ake siyo su a kasuwa
  • Gwamna Ahmed Aliyu zai ƙaddamar da shirin a gidan gwamnatin jihar Sokoto a ranar Laraba, 16 ga watan Oktoban 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Gwamnatin jihar Sokoto za ta fara sayar da kayan abinci na musamman da aka sayo domin ragewa mutane halin raɗaɗin da ake ciki.

Kayayyakin abincin sun haɗa da shinkafa da sauran kayan masarufi waɗanda za a sayar kan ragin kaso 55% cikin 100% kamar yadda gwamnatin ta sanar a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Gwamma ya amince da N77,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata

Gwamnatin Sokoto ta rage farashin shinkafa
Gwamnatin Sokoto za ta siyar da shinkafa kan farashi mai rahusa Hoto: Ahmed Aliyu Sokoto
Asali: Facebook

Babban sakataren yaɗa labaran gwamnan, Abubakar Bawa, ya tabbatar da hakan ga jaridar The Punch a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Sokoto ya kawo sauƙi ga talakawa

Ya bayyana cewa Gwamna Ahmed Aliyu zai ƙaddamar da shirin sayar kayan abincin a gidan gwamnati ranar Laraba.

Ya kuma ce an ware kayayyakin ne domin sayarwa a mazaɓun da ke faɗin jihar domin tabbatar da cewa masu ƙaramin ƙarfi sun amfana, rahoton The Guardian ya tabbatar.

"Za a fara shirin sayar da kayan abincin a gidan gwamnati kuma ina shaida muku da zarar an ƙaddamar za a same su a duk wuraren da aka ware."
"Gwamnan a wani ɓangare na ƙudirinsa na ganin shirin ya kai ga mabuƙata, ya yanke shawarar samar da shi a dukkanin mazaɓu 242 na jihar."
"An ware wasu buhuna ga kowace mazaɓa kuma ana sa ran za a ci gaba da gudanar da shirin har sai al’amura sun daidaita a jihar."

Kara karanta wannan

Mummunar ambaliyar ruwa ta jefa mutane miliyan 2 cikin babbar matsala a Arewa

- Abubakar Bawa

Gwamnatin Sokoto ta zargi PDP da karya

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin Ahmed Aliyu ta jihar Sakkwato ta zargi jam'iyyar adawa ta PDP da yada karya da daukar nauyin rahotannin kage.

Gwamnatin ta ce PDP na fafutukar kawar da hankalin gwamnatin Ahmed Aliyu daga gudanar da ayyukan ci gaba da raya kasa da inganta rayuwar yan Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng