Mutane Kusan 100 Sun Rasu sakamakon Fashewar Tankar Mai a Jigawa
- Wata tankar mai ɗauke da man fetur ta gamu da tsautsayi a ƙaramar hukumar Taura ta jihar Jigawa a makon nan
- Tankar ta faɗi bayan ta ƙwacewa direban da yake tuƙata a ƙauyen Majiya a cikin tsakar daren ranar Talata
- Mutanen ƙauyen sun fara ɗiban man fetur ɗin da yake cikin tankar kafin daga bisani ta kama da wuta a rasa rayuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Jigawa - Kusan mutane 100 ne suka bar duniya sakamakon faɗuwar da wata tankar mai ta yi a jihar Jigawa.
Faduwar tankar man wanda ya auku a ƙauyen Majiya da ke ƙaramar hukumar Taura ya kuma yi sanadiyyar raunata mutane sama da 50.
Tankar mai ta faɗi a Jigawa
Jaridar The Nation ta rahoto cewa tankar mai ɗauke da man fetur ta faɗi ne da misalin ƙarfe 12:30 na daren ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutanen ƙauyen dai sun garzaya zuwa wajen domin ɗibar man feturin kafin tankar ta kama da wuta.
Ƴan sanda sun yi ƙarin bayani
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Jigawa, DSP Lawal Shiisu Adams ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.
"Wata tankar mai da ta taho daga Port Harcourt zuwa Nguru a jihar Yobe ta isa ƙauyen Majiya da ke ƙaramar hukumar Taura da misalin ƙarfe 12:30 na dare. Motar ta ƙwacewa direban a Majiya wanda hakan ya sanya ta faɗi."
"Abin da ke cikin tankar ya cika magudanun ruwa da ke a ƙauyen. Mutanen ƙauyen sun fara ɗiban man fetur ɗin kafin daga bisani ya kama da wuta."
"A sakamakon haka an tabbatar da rasuwar mutane 95 sannan an kwantar da mutane 50 a asibiti."
- DSP Lawan Shiisu Adam
Kotu ta takawa VIO burki
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta haramtawa jami'an hukumar VIO dakatar da ababen hawa, kwace masu motoci ko cin tarar direbobin.
Ana ganin wannan sabon hukuncin da kotun ta yi zai kawo babban sauyi ga yadda hukumar VIO ke gudanar da ayyukanta a kan titunan kasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng