Sojoji Sun Bindige 'Yan Bindigan da Suka Je Karbar Kudin Fansa
- Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wasu ƴan bindiga mutum biyu har lahira a jihar Kaduna
- Sojojin sun sheƙe ƴan bindigan ne lokacin da suka je ɗaukar kuɗin fansa na wasu mutum huɗu da aka dauke
- Sojojin sun yi wa ƴan bindigan shigo-shigo ba zurfi ne wanda hakan ya sanya suka samu nasarar hallaka su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Sojoji sun bindige wasu ƴan bindiga guda biyu a lokacin da suke ƙoƙarin karɓar kuɗin fansa a jihar Kaduna.
Ƴan bindigan dai sun je karɓar N1.5m a matsayin kudin fansar mutane huɗu da suka sace a ƙauyen Mai-Iddo da ke ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa sojojin sun kuɓutar da mutanen huɗu da suka haɗa da mata uku da yaro ɗaya, waɗanda aka yi garkuwa da su a wata gona a makon jiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda sojoji suka kashe ƴan bindigan
Shugaban al’ummar yankin ya tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho a ranar Talata, 15 ga watan Oktoban 2024.
Ya ce an kashe ƴan bindigan ne bayan shugabansu ya umarce su da su je wani wuri da aka tsara cewa ɗan uwan mutanen da aka sace zai ajiye kuɗin fansan.
"An kammala shirye-shirye tsakanin sojoji tare da mutumin da zai kai musu kuɗin fansa da kuma ɗan banga. Da isa wurin, sai sojojin suka ɓoye."
"Yayin da biyu daga cikin ƴan bindigan suka fito domin karɓar kudin fansan, sai sojojin suka buɗe musu wuta tare da hallaka su nan take."
- Wani shugaban al'umma
Ya ƙara da cewa sojojin sun kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su tare da sake haɗa su da iyalansu.
Wane bayani ƴan sanda suka yi?
Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan wannan lamarin ba.
Kakakin ƴan sandan bai ɗauki kiran wayar da aka yi masa ba sannan bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.
Ƴan bindiga sun harbi shugaban rundunar tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun harbi darakta janar na rundunar Askawaran Zamfara (CPG), Janar Lawal B. Muhammad (mai ritaya).
Ƴan bindigan sun harbi Janar Muhammad ne a lokacin da suka kai hari kan masu ababen hawa a ƙauyen Kucheri da ke ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng