Gwamna a Arewa Ya Fadi Gaskiya kan Shirin Rusa Fadar Sarki da Masallacin Juma'a

Gwamna a Arewa Ya Fadi Gaskiya kan Shirin Rusa Fadar Sarki da Masallacin Juma'a

  • Gwamnan Taraba ya musanta zargin cewa gwamnatinsa na shirin rusa fadar Takum da babban Masallacin Juma'a a garin
  • Kwamishinar yaɗa labarai, Zainab Usman Jalingo ta ce zargin ba shi da tushe, inda ta bukaci mutane su yi watsi da shi
  • Tun farko dai kungiyar Kuteb ta Najeriya watau KYN ta zargi gwamnatin Agbu Kefas da yunkurin rusa wuraren na tarihi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Taraba - Gwamnan Agbu Kefas na jihar Taraba ya musanta shirin rusa fadar sarkin Takum da babban Masallacin Juma'a na garin.

Gwamna Kefas ya bayyana zargin da aka ɗorawa gwamnatinsa cewa za ta rusa muhimman wuraren biyu da tsagwaron ƙarya.

Gwamna Agbu Kefas.
Gwamnatin Taraba ta musanta zargin tana shirin rusa fadar Takum da babban Masallacin Juma'a Hoto: Agbu Kefas
Asali: Twitter

A rahoton Daily Trust, kwamishinar yada labarai ta jihar, Zainab Usman Jalingo, ta ce irin wadannan zarge-zarge ba su da tushe balle makama.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta dakatar da tsohon mataimakin gwamna da wasu mutum 6

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ƙara da cewa an kirkiro wannan karyar ne domin harzuƙa mutanen garin Takum da nufin ta da zaune tsaye.

Kungiyar Kuteb ta zargi gwamnatin Taraba

Idan ba ku manta ba kungiyar bunƙasa al'adun kabilar Kuteb ta Najeriya (KYN) ta yi zargin gwamnatin Taraba na shirin rusa fadar Takum da Masallacin Juma'a.

Shugaban ƙungiyar, Mr. Emmanuel Ukwen ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Jalingo, babban birnin jihar, rahoton Tribune Nigeria.

Ya ce an fara zaman ɗar-ɗar da fargaba a garin bayan samun labarin shirin gwamnati na rusa fada da Masallacin, inda ya ce hakan zai haifar da sabon rikici.

Gwamnatin Taraba ta maida martani

Da take mayar da martani, kwamishinar yaɗa labarai, Zainab Usman ta ce babu kanshin gaskiya a wannan zargin.

"Gwamnatin Taraba ta maida hankali wajen gina shugabanci nagari wanda zai amfani talakawa ba tare da la'akari da banbancin addini ko ƙabila ba.

Kara karanta wannan

Ana zargin gwamna a Arewa na shirin rusa fadar sarki mai tarihi da Masallacin Juma'a

"Marasa kishi da ke kokarin kawo hargitsi ne ke yaɗa irin waɗannan karerayin, don haka muna kira ga mutanen Taraba su yi fatali da wannan jita-jita," in ji ta.

Kwamishinar ta jaddada cewa gwamnatin Taraba ta himmatu wajen samar da zaman lafiya, ci gaba, haɗin kai walwala da adalci ga kowa.

Masarautar Takum ta koka kan rashin tsaro

A wani rahoton kuma mai sarautar gargajiya a Takum da ke jihar Taraba, Sopiya Ahmadu Gboshi ya nuna damuwa kan rasa rayuwa a yankin.

Basaraken ya zargi yan yankin karamar hukumar Katsina-Ala da ke jihar Benue da ba da gudunmawa wajen rashin tsaro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262