An Kori Yan Sanda kan Kitsa Kashe Dalibi yayin Zanga Zangar Tsadar Rayuwa
- Rundunar yan sandan jihar Kwara ta fitar da rahoton bincike kan zargin wasu jami'ai da aka yi da kisan wani dalibin makaranta
- An zargi yan sanda uku da hannu wajen kisan dalibi mai suna Qoyum Abdulyekeen Ishola yayin zanga zangar tsadar rayuwa
- Rahoton da rundunar yan sanda ta fitar ya nuna can samu jami'an da laifi kuma za a dauki wani mataki bayan korarsu daga aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kwara - Rundunar yan sandan Najeriya ta kori wasu jami'anta guda uku da aka samu da kaifi kan kisan wani dalibin kwaleji.
Dalibin da aka kashe yana karatu ne a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kwara kuma yana shekara ta biyu ne a matakin karatu.
Jaridar Punch ta wallafa cewa binciken yan sanda ya tabbatar da samun jami'an da laifi wajen kisan dalibin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka kashe dalibi lokacin zanga-zanga
A ranar 4 ga watan Oktoba da ya wuce ne aka zargi yan sanda uku da hannu wajen kisan Qoyum Abdulyekeen Ishola yayin zanga zanga.
Lamarin ya jawo suka ga rundunar yan sanda kuma kungiyar dalibai a kwalejin kimiyya da fasaha ta Kwara ta yi zanga zanga kan kisar.
An kori yan sanda kan kisan dalibi
Rundunar yan sanda a jihar Kwara ta fitar da rahoton da ya nuna samun jami'anta uku da kitsa kisan dalibin kwaleji.
Biyo bayan haka, rundunar yan sanda ta tabbatar da korar jami'an su uku daga aiki nan take.
Za a gurfanar da yan sanda a gaban kotu
Leadership ta wallafa cewa za a gurfanar da yan sandan uku a gaban kotu domin yanke musu hukuncin da ya dace.
Kakakin yan sanda a jihar Kwara ya ce matakin da aka dauka na cikin ƙoƙarin tabbatar da adalci da IGP Kayode Egbetokun ya ke yi.
Yan bindiga sun kashe DPO a Delta
A wani rahoton, kun ji cewa wata rundunar yan sanda ta hadu da tsautsayi yayin artabu da yan bindiga a wani yanki na jihar Delta.
Lamarin ya faru ne a safiyar ranar Litinin da ta wuce wanda dan sanda mai matsayin DPO ya rasu da wasu tarin jami'ai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng