Rundunar Yan Sanda Ta Bude Kofa, An Fara Karbar Masu Korafi kan Jami'ai a Kano

Rundunar Yan Sanda Ta Bude Kofa, An Fara Karbar Masu Korafi kan Jami'ai a Kano

  • Rundunar yan sandan kasar nan ta umarci dukkanin jihohi da su bude hanyar karbar korafin jama'a kan jami'ansu bisa yadda su ke aiki
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar reshen jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce tuni aka samar da hanyar karbar korafin
  • Ya shawarci jama'a su kira layukan waya da aka samar ko su yi tattaki zuwa ofishin rundunar domin mika kokensu idan an bata masu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Rundunar yan sandan Kano ta ce a shirye ta ke wajen inganta alaka da jama'a domin kara samun nasara a yaki da ayyukan bata-gari a jihar.

Kara karanta wannan

An kori yan sanda kan kitsa kashe dalibi yayin zanga zangar tsadar rayuwa

Wannan dalili ya sa rundunar ta samar da wani sabon tsari na karbar koken mazauna Kano, musamman wadanda ke zargin jami'anta da aikata ba daidai ba.

Police
Yan sandan Kano sun fara karbar korafi kan jami'ansu Hoto; Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

A sakon bidiyo da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce Sufeton janar na yan sanda Kayode Egbetokun ya umarni da haka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan sanda za su karbi korafin jama'a

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa rundunar yan sandan Kano ta bude ofishin karbar korafin jama'a kan jami'an da ke gallaza masu.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana matakin, inda ya ce an samar da lambobin waya domin karbar wasu korafe-korafen.

Dalilin fara karbar korafi kan yan sanda

Rundunar yan sandan kasar nan ta ba dukkanin ofishoshinta na jihohi umarnin su fara karbar korafin jama'a kan jami'anta domin inganta aiki.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun farauto gawurtattun yan fashi da makami

A sakon da jami'in hulda da jama'a na rundunar reshen Kano, SP Kiyawa ya fitar, ya ce karbar korafin zai taimaka wajen inganta aiki da tabbatar da jami'ai sun yi abin da ya dace.

Kano: Yan sanda sun tsaurara sintiri

A baya mun wallafa cewa kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Garba Salman Dogo ya bayar da umarni ga jami'an rundunar da su tsaurara sintiri domin magance matsalar tsaro.

Salman Dogo ya kuma ba jami'an umarnin amsa duk wani kiran neman agaji da jama'ar gari za su yi ma su, domin ta haka ne za a dakile ayyukan bata gari fadin jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.