Aminu Vs Sanusi II: Rikicin Sarautar Kano Ya Dawo, Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Yi Magana

Aminu Vs Sanusi II: Rikicin Sarautar Kano Ya Dawo, Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Yi Magana

  • Kotun ɗaukaka ƙara za ta fara zaman sauraron kararrakin da aka shigar gabanta kan rigimar sarautar Kano ranar 17 ga watan Oktoba
  • Wannan dai na zuwa ne yayin da Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II ke ci gaba da nuna kansu a matsayin sarakuna
  • An fara rigima kan sarautar Kano ne bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rusa masaurautu biyar kuma ya dawo da Muhammadu Sanusi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta sanya ranar fara zaman sauraron kararrakin da aka shigar gabanta kan rikicin sarautar Kano.

Kotun ta sanar da cewa za ta fara sauraron ƙararrakin da aka ɗaukaka zuwa gabanta game da rikicin sarautar Kano a ranar 17 ga watan Oktoba, 2024.

Kara karanta wannan

Ana zargin gwamna a Arewa na shirin rusa fadar sarki mai tarihi da Masallacin Juma'a

Aminu da Sanusi II.
Kotun daukaka kara za ta fara sauraron shari'ar rikicin sarautar Kano Hoto: Masarautar Kano
Asali: Facebook

Kwamitin alkalai uku karkashin mai shari'a Mohammed Mustapha ne ya zabi ranar fara zaman a jiya Litinin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarautar Kano: Kotun ɗaukaka ƙara za ta fara zama

Ƙararraki biyu da aka ɗaukaka zuwa gaban kotun ɗaukaka kara sun haɗa da ƙara mai lamba CA/KN/166/M/2014 tsakanin sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da Antoni-Janar da wasu 10.

Sai kuma ƙara mai lamba CA/KN/126/M/2024 kan naɗin sarkin Kano tsakanin majalisar dokokin jihar Kano da Alhaji Aminu Babba Dan Agundi da wasu shida.

Har yanzun dai rikicin sarautar Kano ya ƙi ci ya ƙi cinyewa tun bayan dawo da Muhammadu Sanusi II a matsayin sarki na 16.

Aminu Ado Bayero ya ci gaba da zaman fada a ƙaramar fadar Nassarawa, yayin da Muhammadu Sanusi II ke zama a fadar Ƙofar Kudu.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Yadda dan tsohon gwamnan Kaduna ya rasu a hatsarin mota

Kotuna biyu sun ci karo kan sarautar Kano

Idan ba ku manta ba babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta soke matakin Gwamna Abba Kabir Yusuf na tsige Aminu Ado da maido da Sanusi II a watan Mayu.

Kotun ta kuma yi watsi da dokar da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da ita wanda ta rusa masarautun Kano 5 ciki har da kujerar Aminu Ado.

Haka nan kuma babbar kotun jihar Kano ta haramtawa Aminu Ado bayyana kansa a matsayin sarki, lamarin da ya ci karo da hukuncin kotun tarayya.

A halin yanzu rigimar ta kai gaban kotun ɗaukaka ƙara kuma za a fara zaman shari'ar ranar 17 ga watan Oktoba, kamar yadda Sahara Reporters ta rahoto.

Nuhu Ribaɗu ya faɗi sarkin Kano a taro

A wani rahoton kuma mutane sun ɓarke da tafi a lokacin da mai ba da shawara kan tsaron ƙasa, Nuhu Ribaɗu ya kira Aminu Ado Bayero da sarkin Kano.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun harbi shugaban rundunar Askarawan Zamfara, an samu bayanai

Rahotanni sun nuna lamarin ya faru ne a wurin wata lacca da aka shirya a birnin tarayya Abuja ranar Alhamis.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262