Mummunar Ambaliyar Ruwa Ta Jefa Mutane Miliyan 2 cikin Babbar Matsala a Arewa

Mummunar Ambaliyar Ruwa Ta Jefa Mutane Miliyan 2 cikin Babbar Matsala a Arewa

  • Ambaliyar ruwa ta ci garuruwa da dama a kananan hukumomin jihar Kogi, kimanin mutane miliyan biyu sun rasa gidajensu
  • Gwamnatin jihar Kogi ta buƙaci a kawo mata ɗauki domin tallafawa waɗanda wannan mummunan ibtila'i ya rutsa da su
  • Kwamishinan yaɗa labaran jihar, ya roki gwamnatin tarayya da ƙungiyoyin agaji na duniya su taimakawa Kogi a halin yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Gwamnatin Kogi ta bayyana cewa kimanin mutane miliyan 2 ne suka rasa matsugunansu sakamakon mummunar ambaliyar da ta afku a garuruwa 200.

Gwamnatin ta sake yin kira a karo na biyu ga gwamnatin tarayya da ƙungiyoyin agaji na gida da waje su kawo wa jihar ɗauki domin tallafawa waɗanda lamarin ya shafa.

Kara karanta wannan

Soke hukumar EFCC: Gwamna ya saba da takwarorinsa, ya ba da shawara

Gwamna Ahmed Ododo.
Kimanin mutane miliyan 2 sun rasa wurin zamansu sakamakon ambaliya a Kogi Hoto: Alhaji Ahmed Usman Ododo
Asali: Facebook

Kwamshinan yaɗa labarai, Hon. Kingsley Fanwo ne ya faɗi haka a taron manema labarai a garin Katonƙarfe ranar Litinin, Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ambaliya ta ci gidaje a Kogi

Fanwo ya bayyana cewa ibtila'in ya shafi ƙananan hukumomi tara cikin 21 na jihar, hakan ya sa suka buɗe sansanonin ƴan gudun hijira 68.

"Yanzu da nake magana da ku ambaliya ta yi ɓarna a kananan hukumomi tara cikin 21, mun buɗe sansanoni 68 amma ba za su ɗauki dandazon mutanen da suka rasa gidajensu ba.
"Makarantu, asibitoci da wasu gine-gine sun ruguje sakamakon ambaliyar, mutane manya da kananan yara sun wayi gari cikin mawuyacin hali abin tausayi.
"Ba a rasa ko mutum ɗaya ba saboda mun ankarar da mutane tun da wuri. Muna kashe makudan kudi kullum amma ba su zuwa ko ina, muna kira ga gwamnatin tarayya ta kawo mana agaji.

Kara karanta wannan

IGP ya tuna da iyalan 'yan sandan Kano da suka rasu a hatsarin mota

- Kingsley Fanwo.

Gwamnatin Kogi ta fara ɗaukar matakai

Kwamishinan ya ce gwamnatin Kogi ta kafa kwamiti karkashin jagorancin mataimakin gwamna domin tattara bayanai da tallafawa waɗanda ambaliyar ta shafa.

Kananan hukumomi bakwai da suka haɗa da Kogi, Lokoja, Adavi, Ofu, Ajaokuta, Idah, da Ibaji na daga cikin waɗanda ambaliyar ta shafa, Daily Trust ta ruwaito.

Ambaliya: Gwamna Zulum ya fara raba tallafi

A wani rahoton kuma, Gwamna Babagana Umaru Zulum ya kaddamar da fara rabon kayan tallafi ga waɗanda ambaliya ta yi wa barna a Borno.

Zulum ya bayyana yadda aka raba mutanen da ibtila'in ambaliyar ya shafa rukuni rukuni gwargwadon asarar da kowane magidanci ya yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262