Sukar Tinubu: Kalaman Sanatan APC Na Neman Kara Sanya Shi Cikin Matsala

Sukar Tinubu: Kalaman Sanatan APC Na Neman Kara Sanya Shi Cikin Matsala

  • Jam'iyyar APC mai mulki ba ta ji daɗin yadda Sanata Ali Ndume ya fito bainar jama'a yana sukar shugaba Bola Tinubu ba
  • APC ta bayyana cewa kamata ya yi sanatan mai wakiltar Borno ta Kudu ya keɓe da shugaban ƙasan domin ya ba shi shawarwari
  • Ta bayyana cewa ya kamata Ndume ya riƙa tauna kalamansa kafin ya fito ya faɗe su a bainar jama'a a matsayinsa na babba a APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta shawarci tsohon mai tsawatarwa na majalisar dattawa, Ali Ndume, da ya riƙa ba Bola Tinubu shawara a keɓe.

Jam'iyyar APC ta ce hakan zai fi maimakon sukar manufofi ko ayyukan gwamnati a bainar jama’a.

Kara karanta wannan

2027: Tsohon gwamnan PDP ya shawarci Atiku ya hakura da takara, ya fadi dalili

APC ta kunnen Ali Ndume
APC ta ja kunnen Ali Ndume kan sukar Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Senator Muhammad Ali Ndume
Asali: Facebook

Daraktan yaɗa labarai na jam’iyyar APC na ƙasa, Bala Ibrahim, ya bayar da wannan shawarar a ranar Lahadi a wata hira da ya yi da jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta ba Sanata Ali Ndume shawara

Ya ce duk da cewa kowa na da ƴancin faɗin albarkacin bakinsa a tsarin dimokuradiyya, ya kamata jiga-jigai irinsu Ndume su riƙa tauna kalamansu kafin su faɗe su a bainar jama'a.

Hakan na zuwa ne dai bayan Sanata Ndume, mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya magance wahalhalun da ƴan ƙasar nan ke ciki tun kafin lokaci ya ƙure.

Ko APC za ta hukunta Ndume kan sukar Tinubu?

Da aka tambaye shi ko jam’iyyar APC mai mulki ta damu da sabuwar shawarar da Ndume ya ba shugaban ƙasa, Bala Ibrahim, ya ce Ndume na buƙatar ya yi taka tsantsan.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun dauki mataki bayan matashi ya cinnawa kakarsa wuta a Jigawa

"A tsarin dimokuradiyya, mutane na da ƴancin samun ra'ayinsu tare da bayyana shi ba tare da wani ya hana su ba. Ali Ndume na ɗaya daga cikin masu ba shugaban ƙasa shawara."
"Idan kun kasance jam’iyya ɗaya da shugaban ƙasa, dole ne ka ba shi shawarwari domin yana aiki ne a kan manufofi ko manufar jam’iyyar."
"Mutane da yawa suna mutunta Ndume. Domin haka dole ne a ko da yaushe ya tauna maganarsa domin tsoron ka da a yi masa mummunar fassara."
"Amma ina so na yi amanna cewa yana yin hakan ne da zuciya ɗaya. Ko APC ba ta ji daɗi ba ko kuma za ta duba yiwuwar hukunta shi, jam'iyyar ita ta san abin da za ta yi."

- Bala Ibrahim

Jagora a APC ya ba Ganduje wa'adi

A wani labarin kuma, jun ji cewa jagora a APC, Alhaji Saleh Zazzaga, ya ba shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, wa'adin kwanaki bakwai ya sauka daga kan muƙaminsa.

Kara karanta wannan

Soke hukumar EFCC: Gwamna ya saba da takwarorinsa, ya ba da shawara

Wannan sabon yunƙurin na Alhaji Saleh Zazzaga na zuwa ne biyo bayan rashin nasarar da ya yi a kotu kan ƙarar neman a tsige Abdullahi Ganduje.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng