Ana Zargin Gwamna a Arewa na Shirin Rusa Fadar Sarki Mai Tarihi da Masallacin Juma'a

Ana Zargin Gwamna a Arewa na Shirin Rusa Fadar Sarki Mai Tarihi da Masallacin Juma'a

  • Ƴan ƙabilar Kuteb sun nuna damuwa kan shirin rusa gidan sarautar Ukwe da babban Masallacin Jumu'a na yankin a Taraba
  • Ƙungiyar KYN ta zargi gwamnatin Taraba da shirin rusa muhimman wuraren masu kunshe da ababen tarihi da al'adun Kuteb
  • Bisa wannan ne ƙungiyar ta roƙi Gwamna Agbu Kefas da jami'an tsaro su dakatar da shirin domin gudun sake ɓarkewar rikici

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Taraba - Ƙungiyar ƴan ƙabilar Kuteb ta Najeriya (KYN) ta zargi gwamnatin Taraba karkashin Gwamna Agbu Kefas da shirin rusa fadar sarkin Ukwe.

KYN mai rajin kare al'adun Kuteb ta kuma zargi gwamnatin Taraba da yunƙurin ruguza babban Masallacin Jumu'a na garin Ukwe.

Gwamna Agbu Kefas.
Kungiyar KYN ta zargi gwamnain Tarayya da shirin rusa fada da Masallacin Juma'a Hoto: Agbu Kefas
Asali: Facebook

Shugaban ƙungiyar, Mr. Emmanuel Ukwen ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Jalingo, babban birnin jihar, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun harbi shugaban rundunar Askarawan Zamfara, an samu bayanai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

KYN ta hango yiwuwar ɓarkewar rikici

Ya ce an fara zaman ɗar-ɗar da fargaba a garin bayan samun labarin shirin gwamnati na rusa fada da Masallacin, inda ya ce hakan zai haifar da sabon rikici.

Mista Emmanuel Ukwen wanda ya samu wakilcin Markus Apwende ya ce wasu makiyan zaman lafiya ne ke kulle-ƙullen yadda za su harzuƙa ƴan kabilar Kuteb.

Ya kuma yi zargin cewa a ranar Juma'a an ga wani bature tare da jami'an tsaro da ƴan baranda yana shafa alamar za a rusa fadar Takum da babban Masallaci.

"An gina fadar tare da babban masallacin tun 1912 kuma wurin na tattare da ƙaburburan manyan sarakunan Ukwe Takum waɗanda suka mutu a kan karagar sarauta kuma aka birne su a fadar.
"Wannan gidan sarauta na kunshe da kayan tarihi da al'adu masu matuƙar muhimmmanci ga ƴan ƙabilar Kuteb tare da wasu kayayyaki da bai kamata a taɓa su ba," in ji Ukwen.

Kara karanta wannan

Soke hukumar EFCC: Gwamna ya saba da takwarorinsa, ya ba da shawara

An roki dakatar da rusa fada da Masallaci

Shugaban KYN ya tunatar da cewa an sha fama da tashe-tashen hankula a yankin Takum kuma al'ummar Kuteb ba za su so wani rikici ya sake barkewa ba, in ji Tribune Online.

A ƙarshe Emmanuel Ukwen ya yi kira ga gwamnatin Taraba da jami’an tsaro da su sa baki tare da dakatar da shirin rushe fadar Ukwe da babban masallacin Juma’a.

Gwamnatin Taraba ta magantu kan tallafin Tinubu

A wani rahoton kuma kun ji cewa gwamnatin jihar Taraba ta fitar da sanarwa kan tallafin shinkafa da gwamnatin tarayya ta ce za ta ba dukkan jihohin Najeriya

Kwamishinan ayyuka na musamman a jihar Taraba, Savior Noku ya ce har yanzu ba su ga alamar shinkafar da aka yi musu alkawari ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262