Lokaci Ya Yi: Yadda Dan Tsohon Gwamnan Kaduna Ya Rasu a Hatsarin Mota

Lokaci Ya Yi: Yadda Dan Tsohon Gwamnan Kaduna Ya Rasu a Hatsarin Mota

  • Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) ta yi ƙarin haske kan hatsarin motan da ya ritsa da ɗan tsohon gwamnan Kaduna, Ahmed Mohammed Makarfi
  • FRSC ta bayyana cewa Faisal Ahmed Mohammed Makarfi ya rasu ne a kan titin hanyar Kaduna zuwa Zaria bayan ya yi hatsari a ranar Asabar
  • Kwamandan FRSC na shiyyar Kaduna ya kuma bayyana cewa sauran mutane biyu da ke cikin motar har yanzu suna a sume

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) ta tabbatar da rasuwar Faisal, ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Mohammed Makarfi.

Faisal ya rasu ne a wani hatsarin mota da ya ritsa da shi a hanyar Kaduna zuwa Zaria a ranar Asabar, 12 ga watan Oktoban 2024.

Kara karanta wannan

An yi rashi: Dan tsohon gwamnan Kaduna ya rasu a hatsarin mota

FRSC ta bayyana yadda dan tsohon gwamnan Kaduna ya rasu
FRSC ta yi bayani kan hatsarin da ya ritsa da dan tsohon gwamnan Kaduna Hoto: FRSC/@HEDankwambo
Asali: UGC

Da yake bayar da ƙarin haske a ranar Lahadi, kwamandan FRSC na shiyyar Kaduna, Kabir Nadabo, ya ce har yanzu wasu mutane biyu da hatsarin ya ritsa da su ba su farfaɗo ba, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda hatsari ya ritsa da ɗan Ahmed Makarfi

Ya ce hatsarin ya faru ne a Lambar Zango da ke kan titin Zaria zuwa Kaduna da ƙarfe 5:15 na yamma, rahoton jaridar Premium Times ya tabbatar.

A cewarsa motar KIA wacce marigayin yake tafiya a cikinta daga Zaria zuwa Kaduna ta rasa tayar gabanta ta dama inda a ƙoƙarin sarrafata ta ƙwace.

Kabir Nadabo ya bayyana cewa tawagar ceto daga RS1.17 a Birnin Yero ta kai ɗauki zuwa wajen.

"Sai dai bayan isa wajen, sun samu labarin cewa mahaifin ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa ya shirya yadda za a kai shi wani asibiti da ba a bayyana ba a Kaduna domin kula da lafiyarsa."

Kara karanta wannan

IGP ya tuna da iyalan 'yan sandan Kano da suka rasu a hatsarin mota

"Saboda haka, tawagar ceto ta kawar da cunkoson da hatsarin ya haifar domin zirga-zirgar ababen hawa. Sai dai daga baya an bayyana cewa ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi ne ya yi hatsarin."
"Bayan isar sa asibitin, an tabbatar da mutuwarsa, yayin da direban da mutum na uku suna a sume har zuwa lokacin da aka kammala haɗa wannan rahoton."

- Kabir Nadabo

Hatsari ya ritsa da ƴan Maulidi

A wani labarin kuma, kun ji cewa aƙalla mutane 36 aka tabbatar sun rasa rayukansu dalilin hatsarin mota a jihar Kaduna a kokarin zuwa Maulidi.

Lamarin ya faru ne a jiya Litinin 16 ga watan Satumbar 2024 a kokarinsu na zuwa Saminaka domin bikin Maulidi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng