Jagora a APC Ya Yabi Ministan Tinubu, Ya Fadi Nasarorin da Ya Samu
- Wani jagora a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ya yabawa ƙaramin ministan tsaro Bello Matawalle kan nasarorin da ake samu kan ƴan bindiga
- Dakta Sani Shinkafi ya bayyana cewa ministan yana matuƙar ƙoƙari domin ganin an kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro
- A cikin ƴan kwanakin nan dai dakarun sojoji sun samu nasarori sosai a kan ƴan bindiga a jihohin Zamfara, Kaduna, Sokoto, Katsina da sauransu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jagoran jam'iyyar APC kuma shugaban ƙungiyar PAPSD, Dakta Sani Shinkafi, ya yabawa ƙaramin ministan tsaro Bello Matawalle.
Dakta Sani Shinkafi ya yabawa ministan kan nasarorin da aka samu a yaƙin da ake yi da ƴan bindiga a jihar Sokoto.
Jagoran na APC ya yabawa ministan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matawalle ya samu yabo
Rundunar sojoji a baya-bayan nan ta yi nasarar fatattakar ƴan ta’adda da dama a faɗin jihohin Zamfara, Sokoto, Kebbi, Katsina, da Kaduna.
"Ƙokarin da sojoji suka yi ya jefa wasu manyan ƴan bindiga irin su Bello Turji cikin ruɗani, lamarin da ya tilastawa da yawa daga cikinsu miƙa wuya ko kuma su yi bankwana da duniya."
"Yunƙurin Matawalle na kawar da waɗannan miyagun la fili yake, tare da maida hankali kan magance matsalolin da suka haɗa da garkuwa da mutane, ƙwace, da tashe-tashen hankula da suka addabi mutanen yankin sama da shekara 15."
- Dakta Sani Shinkafi
Jigon na jam’iyyar APC ya jaddada cewa waɗanda ke zagon ƙasa ga ƙoƙarin sojoji a cikin ƴan siyasa, malamai, ko sarakunan gargajiya suna taimakawa ƴan baindigan ne da gangan.
Ya ce ƙoƙarin da sojojin ke yi na daga cikin manufofin gwamnatin Tinubu na samar da tsaro da zaman lafiya a Najeriya.
Ƙungiya ta nemi afuwar Matawalle
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar APC Akida Forum ta nemi afuwar ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle.
Ƙungiyar ta nemi afuwar ne kan zanga-zangar da suka yi a baya da kuma neman hukumar EFCC ta yi bincike kan lokacin da ya ke gwamnan jihar Zamfara.
Asali: Legit.ng