'Yan Bindiga Sun Harbi Shugaban Rundunar Askarawan Zamfara, an Samu Bayanai
- Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun harbi shugaban rundunar tsaron Askarawan Zamfara a wani hari da suka kai
- Ƴan bindigan sun kai harin ne kan matafiyan da ke bin titin babbar hanyar Gusau zuwa Funtua a ƙauyen Kucheri da ke ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar
- Shugaban rundunar tsaron, Janar Lawal B. Muhammad (mai ritaya) na daga cikin mutanen da harin ya ritsa da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Wasu ƴan bindiga sun harbi darakta janar na rundunar Askawaran Zamfara (CPG), Janar Lawal B. Muhammad (mai ritaya).
Ƴan bindigan sun harbi Janar Muhammad ne a lokacin da suka kai hari kan masu ababen hawa a ƙauyen Kucheri da ke ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.
Ƴan bindiga sun kai hari a Zamfara
Ƴan bindigan sun tare hanyar Gusau zuwa Funtua mai cike da cunkoson jama’a, inda suka farmaki masu ababen hawa ciki har da shugaban rundunar Askarawan Zamfara, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya daga ma’aikatar tsaron cikin gida ta jihar Zamfara, wacce ta buƙaci a sakaya sunanta saboda ba ta da izinin yin magana da manema labarai, ta tabbatar da faruwar lamarin.
Majiyar ta kuma ce shugaban na jinya a wani asibiti da ke Gusau, babban birnin jihar.
"Eh da gaske ne cewa ƴan bindigan sun harbi darakta janar na rundunar Askawaran Zamfara, kuma a halin yanzu yana jinya a asibitin ƙwararru na Yariman Bakura."
- Wata majiya
Harin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da ƴan bindiga suka kashe jami’an rundunar Askawaran Zamfara aƙalla mutane takwas da wani direba a ƙaramar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara.
Me ƴan sanda suka ce kan harin?
Legit Hausa ta nemi jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar domin tabbatar da aukuwar lamarin.
Sai dai kakakin ƴan sandan bai ɗauki kiran wayar da aka yi masa ba kuma bai biyo ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.
Gwamna Dauda ya magantu kan rashin tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya ce ana samun ci gaba kan matsalar tsaro a jihar sakamakon kashe wasu shugabannin ƴan ta’adda.
Gwamna Dauda ya ce duk da cewa gwamnatinsa na yin iya ƙoƙarinta na ganin ta kawar da ƴan bindiga, amma a ƙarshe makomar mutane tana hannun Allah.
Asali: Legit.ng