'Yan Sanda Sun Dauki Mataki Bayan Matashi Ya Cinnawa Kakarsa Wuta a Jigawa

'Yan Sanda Sun Dauki Mataki Bayan Matashi Ya Cinnawa Kakarsa Wuta a Jigawa

  • Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta yi nasarar cafke wani matashi wanda ya cinnawa kakarsa wuta bayan ya watsa mata fetur
  • Jami'an ƴan sandan dai sun cafke matashin ne mai shekara 26 a duniya bayan ya aikata wannan ɗanyen aikin
  • A yayin da ake masa tambayoyi ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa inda ya ce tana yi masa abin da baya so ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Jigawa - Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta kama wani matashi bisa zargin cinnawa kakarsa wuta.

Ƴan sandan sun cafke matashin mai suna Nura Mas'ud mai shekara 26 a duniya da laifin cinnawa kakarwa wuta wacce ta yi sanadiyyar rasuwarta.

Matashi ya cinnawa kakarsa wuta a Jigawa
'Yan sanda sun cafke matashin da ya cinnawa kakarsa wuta a Jigawa Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, DSP Lawan Adam ne ya tabbatar da cafke matashin a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Jagora a APC ya yabi ministan Tinubu, ya fadi nasarorin da ya samu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda matashi ya ƙona kakarsa

Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa lamarin ya auku ne a ranar 8 ga watan Oktoba, 2024, da misalin ƙarfe 4:00 na yamma a ƙauyen Mu’azu, mazaɓar Dan Gwanki, da ke ƙaramar hukumar Sule Tankarkar.

Ya bayyana cewa matashin mai sun Nura Mas’ud ya je gidansu ɗauke da jarkar man fetur wacce ya zubawa kakarsa mai suna Zuwaira Muhammad mai shekara 60 sannan ya banka mata wuta, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa tsohuwar dai daga karshe ta rasu ne a lokacin da aka kwantar da ita a asibiti sakamakon ƙona ta da matashin ya yi.

Ƴan sanda sun cafke wanda ake zargi

Ya kuma ƙara da cewa, tawagar jami’an ƴan sanda reshen Sule Tankarkar sun kama wanda ake zargin tare da tsare shi cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka wasu matasa a harin ta'addanci

"A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amince da aikata laifin da ake zarginsa da shi."
"Wanda ake zargin ya bayyana cewa marigayiyar kakarsa ta ɓata masa rai ta hanyar nuna damuwarta kan yanayin jikinsa da lafiyarsa, wanda shi kuma baya so."

- DSP Lawan Adam

DSP Lawan Adam ya kuma bayyana cewa binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin yana da tarihin tabin hankali kuma yana jinya a asibitin masu taɓin hankali da ke Kazaure.

Ango ya kashe amarya

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani matashin ango ɗan kimanin shekara 30, Motunrayo Olaniyi ya daɓawa sabuwar amaryarsa, Olajumoke wuƙa har lahira a jihar Legas.

Lamarin ya faru ne a rukunin gidajen Amazing Grace Estate da ke Elepe a yankin Ikorodu a jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng