'Yan Bindiga Sun Tare Babbar Hanya a Arewa, Sun Yi Awon Gaba da Matafiya Masu Yawa

'Yan Bindiga Sun Tare Babbar Hanya a Arewa, Sun Yi Awon Gaba da Matafiya Masu Yawa

  • Wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun tare babbar hanyar Gusau zuwa Funtua a jihar Zamfara
  • Ƴan bindigan sun yi awon gaba da matafiya masu yawa bayan sun tare hanyar ranar Asabar, 12 ga watan Oktoban 2024
  • Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce ana ƙoƙarin ceto mutanen da aka sace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun tare babbar hanyar Gusau zuwa Funtua wacce matafiya ke yawan bi.

Ƴan bindigan sun yi awon gaba da wasu matafiya da ba a tantance adadinsu ba bayan sun tare hanyar.

'Yan bindiga sun sace matafiya a Zamfara
'Yan bindiga sun yi awon gaba da matafiya a Zamfara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Tashar Channels tv ta rahoto cewa ƴan bindigan sun tare babbar hanyar ne a tsakanin ƙauyen Kucheri da Magazu a ƙaramar hukumar Tsafe.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka wasu matasa a harin ta'addanci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindigan sun kuma riƙa yin harbi kan mai uwa da wabi bayan sun tare hanyar a ranar Asabar.

Ƴan sanda sun tabbatar da harin

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Legit Hausa.

Kakakin ya ce an yi awon gaba da wasu matafiya da ba a tantance adadinsu ba a yayin harin, inda ya ce jami’an ƴan sanda da sauran jami’an tsaro na ci gaba da ƙoƙarin ceto mutanen da aka sace.

"Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar. Ƴan bindigan sun tare hanyar ne inda suka fara harbi kan matafiya sannan suka yi garkuwa da wasu daga cikinsu."
"Rundunar ƴan sanda tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro suna aiki kafaɗa da kafaɗa domin ganin an ceto mutanen da aka sace."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutane a hare haren da suka kai kauyuka daban daban

- ASP Yazid Abubakar

Ƴan bindiga sun sace mutane

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari a garin Kachia a daren ranar Asabar, 5 ga watan Oktoban 2024 inda suka yi garkuwa da mutane tara.

A cewar mazauna yankin, maharan sun shiga garin ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare inda suka fara harbe-harbe, lamarin da ya firgita mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng