'Yan Bindiga Sun Hallaka Wasu Matasa a Harin Ta'addanci

'Yan Bindiga Sun Hallaka Wasu Matasa a Harin Ta'addanci

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar Plateau da ke yankin Arewa ta Tsakiya
  • Ƴan bindigan a yayin harin da suka kai a wurin wani haƙar ma'adanai sun hallaka wasu matasa mutum huɗu da ke aiki a wajen
  • Shugaban matasan yankin wanda ya tabbatar da aukuwar harin ya bayyana cewa ƴan bindigan sun kuma raunata wasu mutum biyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Ƴan bindiga sun hallaka wasu matasa guda huɗu a wani harin da suka kai a jihar Plateau.

Ƴan bindigan sun kai harin ne a daren ranar Juma'a a ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar Plateau.

'Yan bindiga sun kai hari a Plateau
'Yan bindiga sun hallaka mutum hudu a Plateau Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar The Punch ta rahoto cewa matasan da aka kashe suna aiki ne a wani wurin haƙar ma’adanai a yankin Batura.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutane a hare haren da suka kai kauyuka daban daban

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka kai harin

Ƴan bindigan sun farmake su ne da misalin ƙarfe 9:00 na dare, inda suka kashe mutane huɗu a nan take.

Shugaban ƙungiyar matasan Batura, Sabastine Magit, ya tabbatar da kisan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Sabastine Magit ya ce ƴan bindigan sun kuma raunata wasu mutane biyar a yayin harin kafin su bar yankin.

Shugaban matasan ya bayyana sunayen waɗanda aka kashe a matsayin Bwefuk Musa mai shekaru 21, Klingshak Dickson (21), Promise Joshua (20) da Nyam Abaka (20)

Me ƴan sanda suka ce?

Legit Hausa ta tuntuɓi jami'in hulɗa da jama'a rundunar ƴan sandan jihar Plateau, Alabo Alfred, domin samun ƙarin bayani kan lamarin.

Sai dai kakakin ƴan sandan bai ɗauki kiran wayar da aka yi masa ba kuma bai biyo ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Kara karanta wannan

An rasa rai bayan tashin wani abin fashewa a jihar Delta

Basarake ya rasu a hannun ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa hakimin Kanya da ke ƙaramar hukumar Danko/Wasagu a jihar Kebbi, Alhaji Isah Daya, ya rasu a hannun ƴan bindiga.

Ƴan bindigan dai sun yi garkuwa da Hakimin ne tare da wasu mutane takwas na ƙauyensa a daren ranar Lahadi, 6 ga watan Oktoban 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng