Soke Hukumar EFCC: Gwamna Ya Saba da Takwarorinsa, Ya Ba da Shawara
- Gwamnan jihar Adamawa ya yi maganan kan yunƙurin da wasu gwamnoni ke yi na ganin an soke dokar da ta kafa hukumar EFCC
- Gwamna Fintiri ya bayyana cewa kamata ya yi a yi wa hukumar gyara domin ƙarfafa yadda take gudanar da ayyukanta
- Ya kuma soki yadda gwamnatin tarayya ke karɓe ikon kuɗaɗen da aka ƙwato waɗanda aka sace daga asusun jihohi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Adamawa - Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya yi magana kan ƙoƙarin da wasu gwamnoni ke yi na ganin an soke hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC).
Gwamna Fintiri ya bayyana cewa ko kaɗan bai kamata a soke hukumar EFCC ba, sai dai a ƙara ƙarfafa ta domin ta gudanar da aikinta yadda ya dace.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Hard Copy' a ranar Juma'a, 11 ga watan Oktoban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan ƙarar da gwamnonin jihohi 16 suka shigar a gaban Kotun Ƙoli inda suke ƙalubalantar sahihancin dokokin da suka kafa hukumar EFCC.
Wace shawara gwamnan ya ba da kan EFCC
Jaridar The Punch wacce ta bibiyi hirar ta ce Gwamna Fintiri ya bayyana cewa ba kamata ya yi a soke hukumar EFCC ba.
"A wajena yanzu ba lokaci ne da ya dace na soke hukumar EFCC ba, ko da an kafa ta bisa tsarin doka ko akasin haka. Muna buƙatar ta yi aiki yadda ya dace."
"Ya kamata mu kawar da siyasar da a wasu lokutan ke sanyawa ana iƙirarin hukumar na farautar wasu ne kawai ta ƙyale wasu."
Gwamna Fintiri ya kuma soki yadda gwamnatin tarayya ke iko da kuɗaɗen da aka ƙwato waɗanda aka sace daga asusun jihohi, yana mai cewa hakan ba daidai ba ne.
Tun da farko, gwamnan ya bayyana cewa zai yanke shawarar ko zai shiga ƙarar bayan ya yi nazarin ta tare da Antoni Janar na jiharsa.
EFCC za ta binciki Matawalle
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta yi magana kan zargin karkatar da kuɗaɗen Zamfara da ake yiwa Bello Matawalle.
Hukumar EFCC ta ba da tabbacin cewa za ta gudanar da bincike kan tsohon gwamnan na jihar Zamfara, kan zargin almubazzaranci da kuɗaɗe a lokacin da yake kan mulki.
Asali: Legit.ng