Shugaba Tinubu Ya Zarce Zuwa Wata Kasar daga Birnin Landan

Shugaba Tinubu Ya Zarce Zuwa Wata Kasar daga Birnin Landan

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bar birnin Landan na ƙasar Burtaniya inda yake yin hutun aiki na mako biyu
  • Bola Tinubu ya tafi zuwa birnin Paris na ƙasar Faransa domin gudanar da wasu ayyuka masu muhimmanci
  • Mai ba shugaban ƙasan shawara na musamman kan harkokin siyasa, Ibrahim Kabir Masari ya bayyana hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bar birnin Landan na ƙasar Burtaniya zuwa birnin Paris na ƙasar Faransa.

Ana sa ran shugaban ƙasan zai gudanar da wasu ayyuka masu muhimmanci a birnin na Paris.

Tinubu ya zarce Faransa
Shugaba Tinubu ya zarce zuwa kasar Faransa Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Shugaba Bola Tinubu ya tafi birnin Paris

Babban mai taimakawa shugaba Tinubu na musamman kan harkokin siyasa, Ibrahim Kabir Masari ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

An samu mutumin farko da aka gani da Tinubu a Ingila, ya fadi halin da ake ciki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ibrahim Kabir Masari ya bayyana cewa ya tattauna da shugaban ƙasan a gidansa da ke Landan kafin daga bisani suka wuce zuwa birnin Paris na ƙasar Faransa.

"Yau na samu nasarar kai ziyaga ga shugaban ƙasa Bola Tinubu a gidansa da ke Birtaniya, inda muka yi tattaunawa masu muhimmanci.
"Daga nan sai muka wuce birnin Paris na Faransa domin yin wasu ayyukan masu muhimmanci."

- Ibrahim Kabir Masari

Sai dai, hadimin na Shugaba Tinubu bai bayyana abin da suka tattauna da shugaban ƙasan ba a birnin Landan.

A ranar Laraba 2 ga watan Oktoba ne dai Shugaba Tinubu ya bar Najeriya domin zuwa yin hutun aiki na mako biyu a ƙasar Birtaniya.

Karanta wasu labaran kan Tinubu

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Shugaban PDP ya bayyana masu shan wuya a gwamnatin Tinubu

Shugaban PDP ya magantu kan tsadar rayuwa

A wani labarin kuma, kun ji cewa muƙaddashin shugaban jam'iyyar PDP, Umar Damagum, ya yi magana kan halin ƙuncin da ake ciki.

Umar Damagum ya bayyana cewa ƴan Najeriyan da suka karɓi wani abu suka yi zaɓe a 2023 su ne suka fi shan wahala a yanzu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng