Yan Daba Sun Harbi Shahararren Ɗan TikTok, Sun Sace Masa Gwala Gwalai
- Wani shahararren dan TikTok ya hadu da mummunar ƙaddara yayin da wasu yan daba suka afka masa da harbi da tsakar rana
- Ojesanmi Afeez da aka fi sani da Salo ya hadu da yan dabar ne a Lekki a kusa da wani gidan mai yayin da yake neman man fetur
- An ruwaito cewa a halin yanzu, Salo yana kwance a gadon asibiti yana karɓar magani, an ce lamarin na sa ya yi muni sosai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Legas - Wani shahararren dan TikTok ya hadu da sharrin yan daba yayin da yake kokarin neman man fetur.
An ruwaito cewa yan dabar sun harbi Ojesanmi Afeez a kafa kuma sun yi masa mummunar sata.
Jaridar Punch ta wallafa cewa matashin yana kwace a asibiti yana karɓar magani rai a hannun Allah.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan daba sun harbi dan TikTok
Wasu yan daba da ba a gano su wanene ba sun kai hari kan wani shahararren dan TikTok da aka fi sani da Salo a Legas.
Wata majiya ta ce an yi wa dan TikTok din harbi uku kuma yan dabar sun sace masa sarka mai gwala-gwalai.
An kai dan TikTok asibiti bayan harbi
An ruwaito cewa bayan harbin matashin, an kai shi asibitin Perez Medcare a jihar Legas domin jinya.
Ana raɗe radin cewa daga cikin wuraren da harbin ya same shi akwai kafa kuma an ga jini ya bata gaban motarsa.
Halin da dan TikTok, Solo yake ciki
Vanguard ta wallafa cewa shaidar gani da ido ya tabbatar da cewa Salo na cikin mummunan hali da ake tunanin da kyar ya yi rai.
Wani mutumi da ya bukaci a ɓoye sunansa ya ce da ya je asibiti an hana shi shiga wajen matashin saboda munin halin da yake ciki.
Matasa sun kashe mai gidansu a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa yan sandan Kano ta cafke wasu matasa uku bisa zargin kashe wani magidanci da banka wuta ga gawarsa.
Kakakin rundunar yan sandan Kano, Haruna Abdullahi Kiyawa ya sanar da yadda matasan suka kashe mutumin, suka kona gawar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng