Gobara: Gwamna Ya Cika Alkawari, Abba Ya ba Yan Kasuwa Tallafin N100m
- Gwamnatin jihar Kano ta ja tawagar jaje zuwa Kantin Kwari bayan iftila'in gobarar da ta fada kan wasu shaguna
- Gobarar da ta tashi a yammacin Asabar da ta gabata ta lashe da yawa daga cikin shagunan da ke gidan Inuwa Me Mai
- Abba Kabir Yusuf ya jagoranci tawagar jajen, kuma ya bayar da tallafin miliyoyin Naira ga yan kasuwar don rage radadi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta cika alkawarin da ta daukar wa yan kasuwar Kantin Kwari da iftila'in gobara ya fada masu. A ranar Asabar din da ta gabata ne iftila'in gobara ya fada gidan Inuwa Me Mai da ke layin Bayajidda a kasuwar Kantin Kwari da ke Kano.
Darakta janar kan yada labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarci kasuwar domin mika tallafi.
Gwamna Abba ya ba yan kasuwa tallafin N100m
Jaridar Leadership ta wallafa cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya gana da yan kasuwa a ziyarar ganin irin asarar da su ka tafka saboda gobara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Abba ya ba yan kasuwar tallafin Naira miliyan 100 a madadin gwamnatin jihar domin rage masu radadin asarar biliyoyin da su ka yi.
"Za mu gyara kasuwa:" Gwamna Abba
Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin gyara kasuwar Kantin Kwari domin inganta cinikayya da tsaro yayin kasuwanci.
Abba Kabir Yusuf ne ya dauki alkawarin lokacin da ya ziyarci kasuwar a ranar Alhamis, inda ya ce ana shirin sanya fitilu masu amfani da hasken rana.
Gwamna Abba ya fadi illar gobarar kasuwa
A baya mun wallafa cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi takaicin gobarar da ta tashi a wani sashe na kasuwar Kantin Kwari inda ta jawo gagarumar asara ga yan kasuwa.
A sakon jajensa, gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce lamarin zai kawo cikas ga tattalin arzikin jihar tare da shaida wa yan kasuwar cewa gwamnatin Kano za ta taimaka masu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng