Ambaliya: Bayan Tafka Asara, Gwamnatoci Sun Waiwayi Jama'a

Ambaliya: Bayan Tafka Asara, Gwamnatoci Sun Waiwayi Jama'a

  • Gwamnatin tarayya da hadin gwiwar gwamnatin Jigawa ta yi hobbasa wajen tallafawa wadanda iftila'in ambaliya ya shafa
  • Gwamna Umar Namadi ya jagoranci Ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu wajen raba wasu muhimman kayyaki ga jama'a
  • Daga cikin abubuwan da aka raba akwai kayayyakin abinci iri iri da kudi da aka rika mikawa kowane mutum a wani yankin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Jigawa - Gwamnatocin jihar Jigawa da ta tarayya sun fara duba yadda za a tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ya daidaita daga muhallansu.

Gwamnan jihar, Umar Namadi ya jagoranci raba wasu kayayyakin rage radadin da su ka samar tare da hadin gwiwar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi dalilin kawo manufofin tattalin da suka jawo wahalar rayuwa

Jigawa
Gwamnati ta fara raba kayan agajin ambaliya a Jigawa Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Premium Times ta tattaro cewa an raba kayayyakin ga wadanda su ka shiga mawuyacin hali sakamakon ambaliyar da ta afku a karamar hukumar Sule Tankarkar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta raba tallafin ambaliya a Jigawa

Gwamnatin Jigawa ta jaddada aniyarta na taimaka wa mazauna jihar da ambaliyar ruwa ta yi wa barna, tare da bayyana alhinin halin da jama'a su ka shiga.

Tallafin da aka raba wanda aka samu wani kaso daga gwamnatin tarayya ya samu halartar Ministan kasafi da tsare tsare, Atiku Bagudu.

Ambaliyar Jigawa: Wadanne kayan tallafi aka raba?

Gwamnati ta raba wasu kayayyakin rage radadin ambaliya ga mazauna karamar hukumar Sule Tankarkar domin su ji saukin halin da su ka shiga.

Daga cikin kayayyakin da gwamnati ta bayar akwai buhunan shinkafa kilo 25 da gero, sai taliya rabin kwali, kudi N5000 da buhun masara kilo 25 ga kowane mutum.

Kara karanta wannan

"Duk kanwar ja ce:" Bola Tinubu ya gano yadda za a yaki rashawa a Najeriya

Masu kai agajin ambaliya sun makale

A wani labarin kun ji cewa hukumar bayar da agaji na jihar Borno (SEMA) sun gamu da cikas a hanyarsu ta kai agaji bayan ambaliyar da ta yi barna a Maiduguri.

Shugaban SEMA, Barkindo Mohammed na daga cikin tawagar masu kokarin kai agajin kafin su makale a yankin Gozari, inda ake ganin mutane sun rasa gidajensu da ruwa ya shanye.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.